✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Manoman kifi a Kano na neman tallafin gwamnatin tarayya kan karancin abinci

Kungiyar masu kiwon kifi ta kasa reshen Jihar Kano, ta bayyana irin mayuwacin halin da ’ya’yanta suke fuskanta dangane da tashin gauron zabon farashin abincin…

Kungiyar masu kiwon kifi ta kasa reshen Jihar Kano, ta bayyana irin mayuwacin halin da ’ya’yanta suke fuskanta dangane da tashin gauron zabon farashin abincin kifi da bacewarsa a wurin ’yan kasuwa duk da tsadar da yake da shi.

Kungiyar ta bayyana wannan kalubale a matsayin wata barazana da ka iya kawo karshen noman kifi a jihar.

A wata takarda da aka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Nura Uba Ramadan, ya ce tun daga lokacin bullar annobar cutar coronavirus zuwa karshen shekarar kasuwancin noman kifin ya fara fuskantar barazana.

Kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya da ta shiga lamarinsu wanda hakan ne kadai mafita da za a tallafa wa noman kifi ya ci gaba da dorewa a daidai lokacin da manoman kifin ke hakura sun koma wa wasu harkokin kasuwancin na daban.

Ramadan, ya ce “Daga lokacin bullar Coronavirus da zaman kullen an samu karin akalla kudi N2000 kan kowane buhu na abincin kifi a Jihar Kano kuma duk da haka abincin ya yi karanci.

“Akwai yiyuwar kifayenmu su kankance saboda karancin abincin, wanda hakan ka iya janyo barazanar da dama daga cikin mambobin kungiyarmu su hakura da noman.”

“Mun yi tunanin kara N50 kan kowane kilo amma abokanan huldarmu sun ki amincewa da karin da muka yi.”

“A dalilin haka muka kiran gwamnatin tarayya da ta dubi lamarin nan ta kawo mana dauki,” in ji Nura Ramadan

Ramadan ya kara da cewa tunda gwamnatin tarayya ta gamsu da dakatar da shigo da kifi daga waje, to kuwa akwai bukatar ta tallafa wa masu noman kifin a cikin gida.

Kasancewar Ministan Noma dan jihar Kano ne, kungiyar ta ce tana rokon da ya yi amfani da kujerarsa wajen kafa wani kamfani da zai rika samar da abincin kifi a Jihar Kano.