✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman albasa a Sakkwato sun yi cinikin N4bn a wata biyar

Yace daga watan Afrilu zuwa Agustan bana, manoman albasa a Jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeeriya sun sayar da albasa da kudinta ya kai Naira…

Sakataren Kungiyar Manoman Albasa ta Kasa, Alhaji Aliyu Umar ya ce daga watan Afrilu zuwa Agustan bana, manoman albasa a Jihar Sakkwato sun sayar da albasa da kudinta ya kai Naira biliyan hudu.

Ya fadi haka ne a wurin kaddamar da dashen albasa a kauyen Tunga da ke Karamar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato.

Sakataren ya ce ya fahimci Najeriya ta mayar da hankalinta kan noma saboda tayar da komadar tattalin arzikin kasa.

Ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya kan goyon bayan da take bayarwa wurin farfado da tattalin arziki ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), ta Shirin Anchor Browers.

Ya ce gudunmawar shirin ta kara darajar albasar da ake samu da yawan  gaske.

“Ina son ka sani mun yi amfani da wannan dama don kawo sauyi a wannan bangaren ta fuskar cinikin albasa; Sakkwato ce kan gaba wajen samar da albasa.

“Daga watan Afrilu zuwa Agusta bana mun sayar da albasar da darajarta ta kai Naira biliyan hudu.

“Cutar coronavirus da kuma ambaliya sun shafi harkokin kasuwancinmu wurin samar da sauyin da muke muradi”, inji shi.

Alhaji Aliyu Umar ya yi kira ga ’yan kasuwar albasar da su sanya jarinsu don bunkasa kasuwancinta a kasa.

Jami’in shirin Anchor Borrowers daga CBN, Alhaji Abdullahi Faruk ya ce bankin ya bullo da shirin ne don farfado da aikin gona.

Ya ce shuka sabuwar albasar na nufin bunkasa noma domin babu wani abin da ya fi samar wa manoma iri mai ingannci, kuma da noma ne za a iya korar talauci da rashin aikin yi da ke addabar matasa a Najeriya.

Ya kara da cewar an bullo da shirin ne da zimmar cike gibin da ke tsakanin manoma da masu saya a cikin gida in da dama ta samu a fita da kayan zuwa kasashen waje.

“Shirin muna sa ran ya cike gibin da ake da shi a wajen samar da albasa wadda kusan tan miliyan 1.4 ake samarwa a shekara.

“Ana bukatar tan miliyan 2.5 a shekara, ka ga ke nan akwai gibi na kusan tan miliyan 1.1 muna da tabbaci da wannan lamari za a cika gibin da ake da shi wajen samar da albasa”, inji shi.

Ya ce kasuwar albasa tana girma sosai domin kasashe kamar Nijar da Ghana da Burkina Faso da Kwaddibuwa duk sun dogara ne da Najeriya wurin samun albasa.

“Kan haka ya kamata manoman albasa a Najeriya su tashi tsaye don kara bunkasa kasuwar da yawaitar kudin waje a kasa”,  inji shi.

A jawabin Malam Danjuma Ibrahim Shugaban Gonar DAWI ya yi kira ga manoman su yi amfani da damar da suke da ita su fadada noman albasa.