✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman kasar Indiya sun tsunduma yajin aiki

Indiya sun tsaya cik bayan manoman kasar sun fara yajin aiki domin nuna kin amincewar su da wasu dokoki da suka ce na ci musu…

Harkokin sufuri, hanyoyi da kasuwanni a wasu sassa na kasar Indiya sun tsaya cik ranar Talata bayan manoman kasar sun fara yajin aiki domin nuna kin amincewar su da wasu dokoki da suka ce na ci musu tuwo a kwarya.

Yajin aikin dai, wanda ke samun goyon bayan jam’iyyun adawa ya fi tasiri ne a jihohin Punjab da Haryana dake arewacin kasar inda galibin kasuwanni da gidajen mai suka kasance a rufe.

Sai dai a wasu jihohin kuwa an dan sami tirjiya inda wasu kasuwannin da ofisoshi suka ci gaba da hada-hadarsu, duk da dai harkokin sufurin jiragen kasa suma sun fuskanci tasgaro a yankuna da dama na kasar.

Kazalika, manoman da ma wasu jam’iyyun siyasa sun gudanar da gangami a biranen Bangalore da Hyderabad da kuma Kolkata

Manoman dai na bukatar gwamanti ta yi mi’ara koma baya a kan wasu dokoki guda uku da suka shafe su wadanda Majalisar Dokokin Kasar ta amince da su a watan Satumban 2020.

Dubban daruruwan manoman ne dai suka fantsama kan tituna tsawon kwanaki 12 a wani yanki dake da makwabtaka da birnin Delhi, ko da yake ’yan sanda sun taka musu birki daga kokarin su na tsallakawa babban birnin kasar.

Bugu da kari, manoman sun datse kusan dukkan manyan hanyoyin dake dangana wa da babban birnin inda motocin asibiti da sauran masu ayyukan gaggawa kawai ake bari su wuce.

Sai dai gwamnatin kasar karkashin jama’iyyar BJP mai mulki ta ce an kirkiro sabbin dokokin ne da nufin kakkabe ’yan kayi-nayi dake jawo tsadar amfanin gona a kasar.

Manoman sun yi zargin cewa dokar manyan kamfanoni kawai za ta amfana ta hanyar taimaka musu wajen sayen amfani a farashi mai sauki.

Duk yunkurin sasantawar da aka yi tsakanin shugabannin manoman da na gwamnati ya ci tura, har sai nan da ranar Laraba inda ake sa ran dawowa teburin tattaunawa a birnin New Delhi.