✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manomi ya kai karar zomo a Kano

Ana dai zargin zomon ne da yi wa mutane ta'adi

Wani manomi da ke garin Dorawar Sallau a Karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano ya kai karar wani zomo ofishin ’yan bijilan na yankin, saboda yadda yake yi masa ta’adi a gonarsa.

Rahotanni sun ce jim kadan da kai karar ce jami’an suka sa aka yi wa zomon tara-tara, sannan aka cafke shi.

Manomin mai suna Musa Garba ne ya kai karar don neman a shiga tsakaninsa da zomon.

Mamallakin zomon ya ce dama fitinanne ne kuma ya jima yana dauko masa magana ta hanyar yi wa mutane barna.

Ya ce ko a kwanakin baya ma sai da ya shafe kwana da kwanaki bayan ya bar gida kafin ya dawo.

Mai magana da yawun kungiyar bijilante na yankin, Uba Muhammad, ya shaida wa gidan rediyon Dala da ke Kano cewa sun sulhunta manomin da mai zomon, amma bisa sharadin za a kai shi kasuwa a sayar da shi.

Samun rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya dai ba sabon abu ba ne.