✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Manyan jaruman Nollywood 5 da suka fito daga gidajen sarauta

Jaruman sun fito daga gidajen sarauta daban-daban.

Akwai wasu fitattun jarumai a masana’antar fina-finai ta Kudancin Najeriya (Nollywood) da suka fito daga gidajen sarauta.

Duk da haka suna gudanar da rayuwarsu kamar yadda sauran gamagari ke yi, wanda hakan ya sa mutane shakku kan asalinsu.

Aminiya ta tattaro wasu fitattun jaruman Najeriya biyar wadanda mutane ba su san cewa daga gidajen sarauta suka fito ba.

1. Rita Dominic: Fitacciyar jarumar Nollywood ce da ke auren dan jarida, Fidelis Asonike. Mahaifinta basarake ne a Masarautar Waturuocha da ke Karamar Hukumar Aboh Mbais a Jihar Imo.

2. Jide Kosoko: Jide ya shahara a Masana’antar Nollywood, ya fito ne daga gidan iyalan sarautar da ke Jihar Legas.

Jide Kosoko ya fito a fina-finai masu yawa da suka hada da na Ingilishi da Yarbanci. Ya auri mata biyu Karimat da Henrietta, sai dai Henrietta ta rasu a 2016.

3. Omawumi Megbele: Jaruma ce kuma fitacciyar mawakiya wadda ta taba shiga gasar gwada bajintar da aka yi a Yammacin Afirka. Mahaifinta na rike da Masarautar Itsekiri da ke Jihar Delta.

4. King Sunny Ade: Ade ya shahara a bangaren kidan Juju, wanda hakan ne ya sa aka taba yi masa sarautar ‘Omoba’ a Kasar Yarbawa.

Mahaifiyarsa ta fito daga gidan Sarautar Adesida da ke garin Akure, Jihar Ondo, mahaifinsa kuma basarake ne a Masarautar Ondo.

5. Adekunle Gold: Jarumi kuma mawaki, ya auri abokiyar aikinsa, Simi Ogunleye. Shi ma ya fito daga Masarautar Kosoko da ke Tsibirin Legas.