✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan motoci sun tare hanyar Kaduna

Manyan motoci sun tare hanyar shiga garin Kaduna lamarin da ya haddasa gagarumin cunkoson dubban ababen hawa. Wakilinmu ya habarto cewa manyan sun tare hanyar…

Manyan motoci sun tare hanyar shiga garin Kaduna lamarin da ya haddasa gagarumin cunkoson dubban ababen hawa.

Wakilinmu ya habarto cewa manyan sun tare hanyar a daidai unguwar Rigachikun bisa zargin jami’an tsaro tatsarsu da ma’aikata ke yi cewa sai sun ba su cin hanci.

Hakan na zuwa ne bayan a jami’an kula da hanyoyi na Jihar Kaduna (KASTELEA) da wani dan sanda sun lakada wa wasu direbobi duka saboda kin ba su cin hanci na N1,000 a ranar Juma’a da dare kamar yadda suka yi zargi.

Wani direban babbar mota ya shaida wa Aminiya cewa, “Mun tare hanyar ne saboda zaluncin da aka yi wa abokan aikinmu da aka yi musu duka har da rauni saboda sun ki bayar da cin hanci na Naira 1,000”.

Wakilinmu ya iske cunkoson dubban motoci da suka ce tun karfe 9.00 na safiyar Asabar fusatattun direbobin manyan motocin suka tare hanyar da motocinsu masu dauke da kaya.

Da kyar Jami’an kungiyar ma’aikatan sufuri na NURTW da ‘yan sanda daga babban ofishin ‘Yan Sanda da ke Kawo suka lallashi fusatattun fusatattun direbobin suka janye motocin.

Sakataren NURTW Bature Yusuf Suleiman da ya ziyarci wurin ya shaida wa Aminiya cewa direbobin da aka yi wa rauni na samun kulawa a asibiti.

Ya kuma tabbatar cewa, “Daya daga cikin direbobin ya shaida mana cewa wani dan KASTELEA ne ya bukaci direban ya ba shi N1,000 shi kuma ya ki.

“Saboda haka sai dan KASTEA din ya kira wani dan sanda da suke aiki tare, wanda ya sa ice ya fasa gilashin motar saboda direban ya daga gilas. Da direban ya sauko sai dan sandan ya buge shi da sandar a ka, shi ma yaron motar ya samu karaya a hannu”.

Ya ce sakamakon haka ne sauran direbobi suka tare hanyar da motocinsu domin nuna goyon baya ga takwaransu duk da cewa yawancinsu ba ‘yan jihar ba ne.

Ya yi kira da jam’an KASTELEA da su rika bin lalama a mu’amalarsu da jama’a.

Wakilinmu ya tuntubi Janar-Manajan hukumar, Manjo Garba Yahaya, amma ya ce ba zai yi magana ba da jita-jita, sai an kammala bincike domin babu kowa a lokacin da abin ya faru a cikin dare.