Manzon Allah: Haske mai kore duhu (29) | Aminiya

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (29)

 Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina
Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina
    Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa

Yau ma za mu ci gaba da kawo tarihin Shugaban Halitta Annabi Muhammad (SAW):

Munin aika-aikar Bi’iri Ma’un

Baban Barra’u Amir dan Malik ya gabato ga Annabi (SAW) a Madina sai Annabi (SAW) ya kira shi zuwa ga Musulunci sai bai amsa ba kuma bai nisance shi ba, sai dai ya fadi abin da yake buri cewa mutanen Najad za su karba masa idan ya aika musu da masu da’awa. Ya ce ni makwabci ne a wurinsu, sai Manzon Alla (SAW) ya aika musu mutum 70 makaranta sahabbai, sai suka sauka a Bi’iri Ma’unah sai Haram dan Mulham ya je musu da littafi ya ba Amir dan Dufail ko kallon littafin bai yi ba sai ya ba da umarni ga wani mutum ya soke shi ta bayansa, bayan an soke shi ya yi kabbara.

Amir ya nemi taron Bani Amir sai ba su karba masa ba, don suna da makwabtaka da Abu Barra’u, sai ya dawo ya nemi Bani Salim sai suka amsa masa suka kewaye dukkan sahabban nan suka karkashe su, ba wanda ya tsira sai Ka’ab dan Zaid da Amru dan Umayya. shi ma Ka’ab ya yi rauni ne suka dauka ya rasu don ya saje da matattu. Ka’ab ya rayu sai a Yakin Khandak ya yi shahada. Amru kuma sun kama shi da Amir ya ji cewa daga Mudar yake sai ya ’yanta shi a kan wata baiwa da take wurin mahaifiyarsa. Amru ya koma Madina shi kadai, a kan hanyarsa ta komawa ya hadu da wadansu mutum biyu sai ya yi zaton makiya ne ya kashe su alhali bai sani ba, suna da kullin alkawari da Annabi (SAW).

Hakika Manzon Allah (SAW) ya yi bakin ciki mai tsanani da wadannan labarai da ya ji wadanda suka iso a rana daya na kisan sahabbansa da ya faru a watan Safar, Shekara ta 4 Bayan Hijira.

Yakin Banu Nadir

Banu Nadir daya ce daga kabilar Yahudawan Madina sun kitsa mummunan makirci ga Manzon Allah (SAW). Bayan abin da ya faru na kashe mutum biyu na Banu Kilab a kan kuskure da Amru ya yi, Manzon Allah (SAW) ya je wajen Banu Nadir tare da wadansu sahabbansa cikinsu da Abubakar da Umar da Aliyu (Allah Ya kara musu yarda), don su taimaka game da diyyar wadanda aka kashe gwargwadon alkawurran da aka yi da su. Sai suka ce to ya Baban Kasim! Amma ka zauna nan muna zuwa mu biya maka bukatarka, suka kebanta suka yi shawarar wa zai dauki dutse ya hau sama ya jefo shi a kan Annabi (SAW). Sai Amru dan Jihash ya ce shi ne. Manzon Allah (SAW) ya zauna kusa da katanga yana jiransu. Sai Mala’ika Jibrilu (AS) ya sauko ya ba shi labarin abin da suke nufin aikata masa. Sai Annabi (SAW) ya fita daga wurin da saurinsa. Da sahabbai suka riske shi yake labarta musu cin amanar da Yahudawa suka kulla ya kuma tabbatar musu da zai kore su.

Sai ya aika musu Muhammad dan Muslamah ya fada musu su fita daga Madina kada su zauna a cikinta wa’adin kwana goma, duk wanda aka samu bayan wadannan kwanuka za a sare wuyansa. Sun shiga shirin barinta a wasu ’yan kwanuka sai shugaban munafukai Abdullahi dan Ubayyu ya aiko musu cewa “Kada ku fita hakika ina da mutane dubu biyu da za su shiga ganuwarku su yi yaki su mutu saboda ku.”

Kuma Banu Kuraiza za su taimake ku da Gitfan, wannan ya sa suka ji suna da karfi don haka suka yi zamansu suka fasa fita. Suka aika wa Annabi (SAW) cewa ba inda za su, ya yi duk abin da ya ga dama. Manzon Allah (SAW) ya yi kabbara sahabbai ma suka yi, sai ya shugabantar da Abdullahi bn Ummu Maktum a Madina ya bai wa Aliyu (RA) tuta suka tafi suka same su suka mamaye su a cikin ganuwarsu, sai suka labe a jikin ganuwa suna harbin Musulmi da jifansu. Dabinai da gonakinsu sun taimaka musu sosai, sai Annabi (SAW) ya yi umarnin a sassare dabinan da kona su, sai azamarsu ta dakushe, Allah Ya jefa tsoro a zukatansu bayan kwana shida, a wata ruwayar kwana 15 suka sallama a kan za su fita. Ga shi Banu Kuraiza sun juya musu baya, sannan shugaban munafukai kuma ya ha’ince su. Sai suka zama kamar fadar Allah:

“Kamar Shaidan da ya ce ga mutum ‘ka kafirta!’ Yayin da ya kafirce ya ce ‘lallai ne ni na barranta daga gare ka, ni ina jin tsoron Allah Ubangijin talikai.” (Alhashr: 16.)

Annabi (SAW) ya yi musu rangwame su dauki abin da za su iya na guzuri da dukiya amma ban da makami, sai suka dauki abin da za su iya har kofofi da tagogi, turaku da rufi suka rika cirewa suna dora wa rakumansu.

Sun sauka a Khaibara wadansu kuma kasar Sham. Annabi (SAW) ya raba filayensu da gidanjensu ga masu Hijira na farko kebance, haka nan Abu Dajana da Sahlu dan Hanif mutanen Madina ne ya ba su don fakirancinsu, ya ciyar da ahalinsa tsawon shekara a ciki, abin da ya rage na dawaki da makamai ya saka su ta hanyar Allah, an samu garkuwa 50 da takubba 340.

Yakin Badarul Mau’ida

Abu Sufyan ya dauki alkawari a Uhudu a kan zai dawo shekara mai zuwa ya yaki Musulmi, don haka watan Sha’aban na kamawa a shekara ta 4 Bayan Hijira sai Annabi (SAW) ya fita zuwa Badar kamar yadda aka yi alkawari, tare da mayaka 1500. Mahaya doki mutum 10, ya bai wa Aliyu (RA) tuta sannan ya halifantar da Abdullahi dan Rawaha a garin Madina. Da ya isa ya yi kwana takwas a cikinta yana jiran Abu Sufyan, amma shiru.

A daya bangaren shi ma Abu Sufyan ya fito da mayaka 2000 da mahaya 50, da suka kai wani wuri da ake kira Murra Zahran suka sauka don samun ruwa. Abu Sufyan tunda suka fito tsoro ya kama shi don haka sai ya ce musu: Wannan shekarar ba za ta yi muku kyau ba, sai dai shekara mai yabanya wadda kuke kiwata ita ce a cikinta kuma kuke shan madara, wannan dai shekarar bakararriya ce. Lallai ni kam na koma kuma ku koma, sai suka juya babu abin da ya faru a wannan fitowa yaki.

Musulmi sun amfanu a wadannan kwanuka da suke jiran Abu Sufyan, sun sayar da kayan kudin da suke tare da shi na kasuwancinsu kuma suka ci riba, Dirhami biyu kan kowane Dirhami. Duk wani makiyi jiki ya yi sanyi, aminci ya samu a kowane sashe ya kasance tsawon shekara babu wani makiyi da ya yi ja’irci, ko tayar da zaune-tsaye. Manzon Allah (SAW) a wannan tsakani da falalar Allah ya samu damar amintar da iyakoki mafiya nisa, Allah Ya shimfida masa aminci da kwanciyar hankali ya kasance yana fita ya ladabtar da ’yan fashi har zuwa Daumatu Jundul a Rabi’ul Awwal shekara ta 5 Bayan Hijira.