Manzon Allah: Haske mai kore duhu (39) | Aminiya

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (39)

    Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa

Darasi na Arba’in da Shida Yakin Tabuka

Tun lokacin da Rumawa suka tozarta a Yakin Mu’uta duk da dimbin yawansu kuma Musulmi wadanda ba su wuce dubu uku ba suka gagare su, wannan ya yi tasiri a zukatan kabilun Larabawa masu makwabtakar Sham wadanda suke Kirista ne sai suka tashi tsaye suna neman ’yancinsu, sai Rumawa suka ga su ma su tashi su yaki Musulmi a gidajensu a Madina su gama da Musuluncin da mabiyansa. Kabilar Juzam da Lahm da Amila da Gassam da wasu suka yanke shawarar haduwa da sojojin Hirakal kan su kai wannan hari.

Manzon Allah (SAW) da labarin ya kai gare shi, sai shi ma ya tashi ya nemi Musulmi su fito daga ko’ina kuma ya sanar da wurin da za a tafi yaki don mutane su kintsa sosai. A da bai kasance yana sanar da su ba sai dai a yi kamar za a yi wani waje idan tafiya ta nisa a canja hanya, ga shi ana tsananin zafi da yunwa saboda fari. Mafi yawan wadanda suka fito ba su da kudin da za su sayi makami.

Manzon Allah (SAW) ya nemi Musulmi su bayar da abin da Allah Ya hore musu don ciyarwa a tafarkin Allah. Musulmi kuwa suka amsa, Umar (RA) ne ya fara kawowa, yake cewa a ransa “Yau sai ya wuce Abubakar!” Ya kawo rabin dukiyarsa. Da Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi me ka bar wa iyali?”Sai ya ce, “Kamar wanda na kawo nan.”Ma’ana rabin abin da ya mallaka.

Sai ga Abubakar (RA), ya kawo duk abin da ya mallaka gaba daya Dirhami dubu hudu. Sai Annabi (SAW) ya ce masa, “Me ka bar wa iyalinka?”Sai ya ce, “Na bar musu Allah da ManzonSa (SAW)!”

A nan Umar ya fara kuka, ya ce, “Uwata da ubana fansa gare ka ya Abubakar! Duk wuce ka da nake so in yi a wurin ayyukan alheri na fahimci ba zan taba wuce ka ba.”

Usman kuma (Allah Ya kara masa yarda) ya bayar da ayarin da ya loda wa kaya za a tafi masa kasuwanci Sham gaba daya da rakuman da kayan da suke dauke da su: rakumi dari uku, dawaki hamsin, da Dinari dubu. A ranar ne Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wani abin da Usman zai aikata ya cutar da shi bayan yau.”

Abdurrahman dan Awfu (RA) ya bayar da ukiya dari biyu da Dirhami dubu hudu shi ma kamar Umar (RA) ya raba dukiyarsa shi ne da ya ce ya bar rabi ga iyali sai Manzon Allah (SAW) ya yi masa addu’a ga abin da ya bar musu. An ce a dalilin wannan addu’a da ya rasu kowace cikin matansa ta samu gadon Dinari dubu goma sha takwas. Abbas (Allah Ya kara masa yarda) shi ma ya bayar da dukiya mai yawa, haka nan Dalha da Sa’ad dan Ubbada. Asim ya bayar da buhun dabino casa’in, haka dai sahabbai suka yi ta bayar da dukiya don ciyarwa, wadansu ma gwargadon mudu daya zuwa biyu suka rika bayarwa iya karfinsu, har ta kai wadanda ba su da komai suna kuka don ba a samu abin da zai dauke su ba don rashin guzuri su bakwai ne aya ta sauka a kan haka cewa babu laifi a kansu. Bayan nan Usman (RA) ya dauki nauyin mutum uku na abin hawa da guzuri, Abdurrahman (RA) ma ya dauki nauyin biyu sai Dan Umair ya dauki biyu.

Mata su ma sun rika aikowa da kayan kwalliyarsu na zinari, haka nan igiyoyi na daure kaya ko rakumi da duk abin da ake bukata wanda Allah Ya hore musu.

A ranar munafukai suna ta yi da wadanda suka bayar da yawa suna cewa wai riya ce, wadanda kuma suka ba da kadan sun sha izgili a wajensu. Shi kuma Manzon Allah (SAW) suka yi ta sukarsa da tsaurin kai a kan tunkarar Rumawa. Abdullahi dan Ubayyu shugabansu har yana cewa Manzon Allah (SAW) ya dauki Rumawa wani kayan wasa, ga Annabi da Musulmi can ina ganin har an kama su an gama sun zama bayi. Haka har wannan zuga ta munafukai ta yi tasiri, sai suka rika zuwa suna ba da uzururruka na karya wai ba za su samu damar halartar wannan yaki ba. Wajen munafukai 80 suka nemi hanzari, haka nan kauyawa su ma wadansu sun nemi izini sai dai akwai Musulmi masu tsarkakakkiyar niyya da suka nemi izinin tsayawa.

Manzon Allah (SAW) ya wakilta Muhammad dan Maslamah a kan Madina, kuma ya wakilta Aliyu dan Abu Dalib a kan iyalansa. Ya bai wa Abubakar babbar tuta, ya ba Zubair ta Muhajirai, Ussaid dan Hudair ta Awsu, Habbab dan Munzir ta Khazraj. Ya fita ran Alhamis tare da runduna mai yawan mahaya 30,000 suka nufi Tabuka.

Yawan mutanen ya sa karancin guzuri da abin hawa ta yadda mutum goma ne suke tafiya da abin hawa daya a tsakaninsu ga kuma nisa, wannan ya hau, in an jima ya sauka wani ya hau. Ya kasance saboda karancin abinci har suna cin ganyen itatuwa kuma suka bukatu ga yanka rakumi don su sha ruwan da yake ajewa a cikinsa suka yanka suka sha.

Suna kan hanya ce Aliyu (Allah Ya kara masa yarda) ya riske su, dama tunda za su ya so ya yi kokarin aje da shi ba ya son rabuwa da Manzon Allah (SAW) har yana kuka ya ce ya za a bar shi cikin yara da mata? Sai ya lallabe shi ya koma ya ce: “Ashe ba za ka yarda ka zamar mini kamar matsayin Haruna ga Musa ba? Sai dai babu Annabi a bayana!” To bayan ya koma ne kuma sai ya ji munafukai suna cewa Annabi (SAW) ya bar shi ne don ba ya son ya tafi da shi, kuma wai ba ka maraba da ni akwai abin da ka gani ba ka so in kasance cikinsa “Aliyu (RA) yana jin haka shi ne ya sake biyo su ya same su a Jurf a nan ne Manzon Allah (SAW) ya karyata su. Da Aliyu (RA) ya tabbatar da haka sai ya koma Madina, munafukai dama niyyarsu ke nan su kawo rudani a cikin Musulmi.

Bayan mutum uku muminai da suka zauna ba da kwakkwaran uzuri ba, sai ga shi shi kuma Abu Zar ya fito amma an bar shi baya saboda raunin abin hawansa ba ya iya tafiya. Da ya ga abin na nema ya faskara sai ya kyale dabbar ya dauko kayansa a bayansa ya taho a kasa, har sahabbai suna sanar da Manzon Allah (SAW) an bar Abu Zar a baya don rakuminsa ba ya iya tafiya. Sai ya ce idan akwai abu mai kyau tare da ita, Allah zai sa ya same mu.”

A lokacin da suka sauka don su huta sai ga wani sun hango ba su gane ko wane ne ba, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ya jikan Abu Zar! Zai rayu shi kadai, ya rasu shi kadai, kuma a tayar da shi shi kadai, amma wadansu muminai za su yi masa Sallah.”

Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:aliyugamawa@gmail.com