✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (8)

Shi kansa Annabi (SAW) an sha ci masa mutunci da yunkurin lahanta shi. Daga cikin wadanda suka tsananta wa Annabi (SAW) a wannan lokaci, akwai…

Shi kansa Annabi (SAW) an sha ci masa mutunci da yunkurin lahanta shi. Daga cikin wadanda suka tsananta wa Annabi (SAW) a wannan lokaci, akwai Abu Lahab da Abu Jahil da Asi bin Wa’il da Walid Ibn Mughira da Ukba bin Abu Mu’aidin da sauransu. An ruwaito cewa wata rana Ukba bin Abu Mu’aidin ya taho ta bayan Annabi (SAW) ya kama shi ya shake shi shakewa mai tsanani, ya kasa kwacewa har sai da Sayyidina Abubakar (RA) ya je ya ture shi sannan ya ce masa; don me za ku kashe mutum don ya ce abin bautawarsa shi ne Allah Shi kadai? (Bukhari ne ya ruwaito)

Sakamakon haka ne, kamar yadda wadansu malamai suka bayyana, aka saukar da ayoyin da ke cikin Suratul Masad, inda Allah (SWT) Yake cewa:

“Hannaye biyu na Abu Lahabi sun hallaka, kuma shi ma ya hallaka. Dukiyarsa ba ta tsare masa komai ba, da abin da ya tara. Zai shiga wuta mai huruwa. Tare da matarsa, mai daukar itacen wuta. A bisa wuyansa akwai igiyar wuta ta kaba (ranar tashin Alkiyama).”(Suratul Masad:1-5).

Wadannan su ne mabudan gwagwarmayar Manzon Allah (SAW) a garin Makka wadda ya dauki shekara 13 yana yi, ba tare da an samu wata sararawa ba.

Darasi na Goma Sha Uku:

Halin da Musulmin farko suka shiga bayan bayyanar da kiran da Annabi (SAW) ya yi:

Bayin Allah na farko da suka musulunta su ne suka fara dandana azaba da tsangwama daga hannun Kuraishawa a garin Makka. Domin sakamakon kokarin da Annabi (SAW) ya yi na isar da sakon Allah kai-tsaye ga danginsa da kuma mutanen Makka baki dayansu, an yi ta samun daidaikun mutane, musamman daga talakawa da masu rauni, wadanda suke amsa kiransa suna rungumar addinin da aka aiko shi da shi. A dalilin wannan sai shugabanni da masu fada-a-ji suka fara ganin Annabi (SAW) da sabon addininsa a matsayin barazana ga tsarin zamantakewarsu da al’adunsu na Jahiliyya.

Daga cikin irin gwagwarmayar da ya yi a farkon isar da sakonsa, akwai wata rana da Annabi (SAW) ya bayyana a fili, a gaban dakin Ka’aba yana kiran mutane kan su yi watsi da bautar gumaka su koma ga kadaita Allah wajen bautarsu. Sai nan da nan mutane da ke kusa suka kai masa hari.

A wannan lokaci Haris Ibn Abu Halah (dan Ummu Khadija), wato agolan Annabi (SAW) ya kawo masa dauki, wanda a dalilin haka suka rufe shi da duka har suka kashe shi. Haka shi ma Abubakar (RA) ya yi yunkurin bayyana addinin Musulunci a sarari tare da karanta ayoyin Alkur’ani a gaban dakin Ka’aba. Nan take mutanen da suke wurin, irin su Utbah Ibn Rabi’ah, suka yi ca a kansa suka far masa da duka, har sai da suka sumar da shi. Mutanen kabilarsa ta Banu Tayim su suka samu kubutar da shi, amma duk da haka tunda ya suma da safe bai farfado ba sai da dare. Abdullahi bin Mas’ud shi ma abin da ya faru da Abubakar As-Siddik ne ya faru da shi a gaban dakin Ka’aba.

Wannan irin musgunawa da Kuraishawan Makka suka yi ta yi wa duk wanda ya karbi addinin Musulunci sai kara watsuwa take yi kuma ba ta bar yaro ba, ba ta bar babba ba. Ba ta bar dan dangi ba, ba ta bar bawa ba, sannan ba ta bar da ba. Shi kansa Annabi (SAW) an sha ci masa mutunci da yunkurin lahanta shi.

Daga cikin wadanda suka tsananta wa Annabi (SAW) a wannan lokaci, akwai Abu Lahab da Abu Jahil da Asi bin Wa’il da Walid Ibn Mughira da Ukba bin Abu Mu’aidin da sauransu. An ruwaito cewa wata rana Ukba bin Abu Mu’aidin ya taho ta bayan Annabi (SAW) ya kama shi ya shake shi shakewa mai tsanani, ya kasa kwacewa har sai da Sayyidina Abubakar (RA) ya je ya ture shi sannan ya ce masa; don me za ku kashe mutum don ya ce abin bautawarsa shi ne Allah Shi kadai? (Bukhari ne ya ruwaito). Haka ma an dora wa Annabi (SAW) tumbin rakumi a wuyansa a lokacin da ya yi sujudar Sallah, ya kasance cikin wannan hali har sai da ’yarsa Fadimatu (RA) ta zo ta janye masa kazantar da hannunta. Abu Jahil ya rutsa shi a gefen dakin Ka’aba ya yi ta zaginsa tare da yi masa munanan kalamai. Da labari ya ishe Baffansa Hamza Ibn Abdulmuddalib sai hankalinsa ya tashi kuma ransa ya baci har ya je inda Abu Jahil din yake ya fuskance shi da wannan magana cikin bacin rai.

A sanadiyyar haka ne ma har Hamza (wadda yake mutum ne jarumi mai kima a idon mutanensa) ya musulunta. Haka dai daya bayan daya aka rika samun muhimman mutane suna shiga addinin Musulunci, har manyan mutane irin su Umar bin Khattab da Dufail Ibn Amr al-Dawsi da Amr Ibn Abasah da Abu Zarri Al-Ghifari da sauransu. Musuluntar irin wadannan muhimman mutane kuma jarumai ta kawo canji mai amfani na ci gaba wajen yada addinin Musulunci. An ruwaito Abdullahi dan Mas’ud (RA) yana cewa: “Ba mu gushe ba muna madaukaka tun daga lokacin da Umar ya musulunta.” (Bukhari ne ruwaito).