✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maulidi: Koyi da rayuwar Manzo Allah shi ne mafita —Gbajabiamila

Koyi da hakan da kuma aiki da shi zai taimaka wa Najeriya wajen samun matsayi mai girma

Shugaban Majalisar Wakilia, Femi Gbajabiamila, ya yi kira ga Musulmi da su yi koyi da rayuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, a sakonsa na bikin Maulidi ga ’yan Najeriya.

Gbajabiamila ya fadi haka ne wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkar yada labarai, Lanre Lasisi ya fitar a don murnar zagayowar ranar.

Ya yi kira ga Musulmi da su matsa kaimi wajen koyi da rayuwar Fiyayyen Halitta, tsira da amincin Allaha su tabbata a gare shi, da kuma kyawawan dabi’unsa.

Domin hakan zai kyautata dangantaka tsakanin junansu, zai kuma sa su kara kusantar Allah Madaukakin Sarki.

Sannan ya ce, nuna kaunar juna da wanzar da zaman lafiya kamar yadda Manzo mai tsira da aminci Allah ya koyar, na da matukar muhimmanci wajen gina Najeriya domin ta zama ingantacciyar kasa.

Kuma koyi da hakan, da kuma aiki da shi, zai taimaka wa Najeriya a tafiyar da take yi na cimma matsayi mai girma da daukaka, yayin da kasar take shirin gudanar da babban zabe a shekarar 2023.