Maraba da Dakin Karatu na Al-Haram | Aminiya

Maraba da Dakin Karatu na Al-Haram

    Ado Saleh Kankiya

Masu iya magana sun ce “Tafiya mabudin ilimi.” Ranar Laraba 1 ga Janairun  bana, ta same ni ne a birnin Katsina babban birnin Jihar Katsina, inda na je wani dan gajeren hutu, na kasa da mako daya. A waccan rana abokin tafiyata kuma amini Alhaji Muktari Dangana kwararren Akanta kuma shugaban Kamfanin Muktari Dangana & Co. ne ya dauke mu, ni da Alhaji Garba Isah Mani wani aminin da muka tarar a Katsinan, takanas ta Kano zuwa mazaunin wucin-gadi na Dakin Karatu na Al Haram da Gidauniyar Dakin Karatun ta gina a kan Titin J, kusa da rukunin gidaje masu saukin kudi na Goruba da ke Unguwar Turawa wato GRA, Katsina din, ta kuma tare tun a shekarar 2012.

Malam Khalil Ibrahim Kofar Bai, dan Kwamitin Amintattun Gidauniyar Dakin Karatun na Al Haram, shi ya tarbe mu ya kuma kewaya da mu cikin Dakin Karatun mai bene daya, dauke da littattafai sama da kasa na addinin Musulunci iri-iri. Bayan kammala kewayawar, Malam Khalil ya sada mu da Malam Adamu Yusuf Doro, Mukaddashin Sakataren Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Dakin Karatun na Al Haram, wanda ya dauki tsawon lokaci yana bayyana mana tarihin kafuwar Dakin Karatun da yin cikakken bayani a kan irin littattafan da ya kunsa da kokarin da suke kai yanzu wajen ganin Dakin Karatun ya tashi daga wannan mazauni na wucin-gadi, zuwa mazauninsa na dindindin, a cikin GRA din inda tuni aka aza harsashin ginin.

Kamar yadda Malam Adamu ya shaida mana, yau kusan shekara 24, da suka gabata, Alhaji Abdulkadir Bature Kofar Sauri, dan asalin birnin Katsina, a yanzu kuma mazaunin birnin Makkah a kasar Saudiyya, ya fara bude dakin karatun a zaman daki daya cikin wani gida a Unguwar Kofar Sauri. Babban makasudin kafa dakin karatun inji Malam Adamu, bai wuce kamar yadda taken Dakin Karatun na Al Haram yake ba, “Karanta ka Koya,” wato ma’ana a samu cusa akidar yin karatu da koyonsa, musamman tsakanin kananan yara da matasa, ta yadda za su taso da akidar yin karatu da kuma gane karatun, akidar da ake ta kukan ta yi karanci.

Abubuwa suna bunkasa sannu a hankali a tafiyar da Gidauniyar Dakin Karatun na Al Haram, inji Malam Adamu, a shekarar 2012, sai Dakin Karatun ya samu dawowa mazaunin da yake yanzu na kusa da rukunin gidaje masu saukin kudi na Goruba, bisa ga wadatar wuri da aka samu.

Yanzu maganar da ake gidauniyar ta sake samun wani katafaren fili, kafa 200 da 180 (tsawo da fadi), har an aza tubalin gini.

Wannan sabon wuri da ake fata ya zama mazaunin dindindin na Dakin Karatun, a kasa zai kunshi manya-manyan dakunan karatu biyu, wato na maza da mata da ake sa ran kowane a lokaci guda ya dauki masu karatu da bincike da nazarce-nazarce dari biyar-biyar.

A saman benen da ginin zai kasance mai hawa daya, za a samar da babban dakin taro da zai rika daukar akalla mutum 1,000, a lokaci guda, sauran wurin za a samar da ofishoshi. A wani gefe a kasa an shirya samar da shaguna da kantuna don bayarwa haya da ma dakunan saukar baki, don magance kowace irin matsala da ka iya samu daga baki da ka iya halartar wani taro ko zuwa bincike na wani dogon lokaci a Dakin Karatun. Kazalika an shirya gina masallacin maza da mata da Dakin Karatu na kananan yara, har ma da wurin motsa jiki don yara, yayin da ake sa ran sauran filin ya zama haraba, don ajiye ababen hawa da sauran bukatu.

Dukkan wadannan gine-gine an kiyasta za su lakume Naira miliyan 100.

A game da yadda za a tara wannan kudi, tuni Gidauniyar ta bude Asusun neman taimako a Bankin Jaiz mai suna da lambar ajiya kamar haka: Alharam Library Foundation, 0000649203, inda ake neman al’ummar Musulmi a duk inda suke su tallafa wajen ba da tasu gudummawar a cikin wannan aiki na sadaka mai gudana da akalla Naira 100, wanda tuni al’umma suke ta amsa kira wajen mika tasu gudummawar gwargwadon abin da Allah Ya hore masu, su da iyalinsu.

Mai karatu abin da ya sanya na sadaukar da makalar wannan mako a kan Dakin Karatu na Al-Haram da na gano a Katsina, bai wuce irin himma da kokarin da na gani ba daga shi Alhaji Abdulkadir Bature, wanda shi kadai shekara 24 da suka gabata ya fara wannnan gagarumin aikin alheri, da ba kasafai al’ummar Musulmi ke kulawa da aiwatar da shi ba, duk da irin muhimmancin da yake shi wajen ganin bunkasar addinin Musulunci.

Akasarin mutanenmu sun fi mayar da hankali ne wajen gina masallatai da makarantun Islamiyya.

Mai karatu zai yi tambayar wadanne irin littattafai wannan dakin karatu ya kunsa? A takaice duk littafin ilimi na da, da na yanzu da kira’o’in Alkur’ani Mai girma na manyan malaman duniya da na tafsirai da hadisai da Balaga da na Fikihu da na tarihin Musulunci da na Nahawu da kamus-kamus na Larabci da sauran littafan ilimi da mai karatu ya sani ko yake tunaninsu, in Allah Ya so idan ya je Dakin Karatu na Al-Haram da ke Katsina zai same su.

Na samu labari daga mahukunta Dakin Karatun suna shirin kai wa Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ziyarar ban girma, bayan da suka samu labarin zai ziyarci Dakin Karatun nasu, bisa ga samun labarin shi (Dakin Karatun) da kuma niyyar da aka ce ya yi na kafa irinsa, a zaman bai san da na Katsinan ba.

Saura da me? Sai mu yi fata Allah Ya ba da iko ga Musulmi a duk inda suke wajen taimaka wa Gidauniyar Dakin Karatu ta Al-Haram da ke Katsina. Amin summa amin.