✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marasa gaskiya ke komawa APC — Sule Lamido

Tsohon gwamnan Jigawan ya ce lokacin mulkin karba-karba ya wuce.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce rashin gaskiya ke sa wasu gwamnonin jam’iyyar PDP sauya sheka zuwa APC.

Sule Lamido, wanda daya ne daga cikin iyayen PDP ya ce gwamnonin na sauya sheka ne domin su kare kujerunsu saboda sun san cewa suna da kashi a gindinsu.

A wata hira ta musamman da Aminiya ta yi da shi, tsohon Ministan Harkokin Wajen ya ce, “Mukamin suke bi saboda suna ganin PDP ta ba su [dama sun zama] gwamnoni, ta karrama su [amma kuma] suna ganin tun da sun yi laifi suka koma APC domin kare rashin gaskiyarsu.

“Saboda haka, masu yawon [neman] mukami ne ba mutanen ba ne,” inji shi.

Butulci ne fita daga PDP

A cewarsa, tsabar butulci ne ’yan siyasar da PDP ta yi wa riga da wando, alhali su ba kowan kowa ba ne, su juya mata baya har suna zagin ta saboda sun sauya sheka.

“Rashin sanin girman hakki, rashin sanin girman mutunci da yadda aka karrama ka aka mai da kai mutum [ne] ka zo wanda ya mayar da kai mutum shi za ka zaga — a wayi gari shi kake zagi ka koma wurin mai zagin ka.”

Ya PDP za ta yi?

Ya bayyana cewa duk da sauya shekar gwamnonin, hakan ba zai rusa jam’iyyar ba, hasali ma gwamnonin da masu neman mukami da ke ficewa daga cikinta ba su da wani tasiri a siyasance.

“Uwa mai haihuwa, kullum tana haihuwa ai; Me ya sa kafin su zama gwamnoni ba su sauya sheka ba? [Ko] sun sauya sheka?”

“Dukkan masu wannan yawon idan ka zare mukamin mene ne su? Za su yi magana a Najeriya?

“Duk wanda ya koma APC daga PDP ka kalle shi ka kalli jiharsa da garinsu, idan ba don mukamin ba ya isa ya yi magana?

“Saboda haka mukamin ne suke yawo [a kai] don samun biyan bukata.”

Batun mulkin karba-karba

Tsohon gwamnan ya ce maganar mulkin karba-karba tsakanin shiyyoyin Najeriya abu ne da lokacin yin sa ya wuce, muddin so ake Najeriya ta ci gaba.

Ya ce ko a shekarar 1999 da aka bullo da karba-karba, an yi ne don kawo fahimta da lallashin yankin Yarabawa kan zaben 1993 da aka soke.

“Lokacin da aka yi shi ne an yi zabe na ‘June 12’ Abiola ya ci zabe an soke, shi ake ganin kamar mu ’yan Arewa muka hana shi.

“Saboda haka da za a sake komawa mulkin farar hula muka ce shin ya za a yi muga wannan kurjin ko wannan ciwo na ‘June 12’ an yi maganin sa? Shi ne aka ce a kai mulkin nan kasar Yarabawa, A PDP ke nan. Wannan shi ne hikima.

“A wannan lokaci duk jam’iyyun guda uku — AD da PDP da APP — suna da shugabanni masu hikima masu basira masu hangen nesa; Abin da muka yi a PDP ya sa mutanen AD da APP suka ce tunda abokanmu sun yi wannan abu don zaman lafiya mu ma ya kamata mu yi.”

“Wannan ya sa a wancan lokacin duk ’yan takarar suka fito daga kasar Yarabawa.

“An yi ne saboda hikimar wancan lokacin domin muna da shugabanni masu adalci, masu hangen nesa, masu cewa a yi maganin ciwon da ke damun Najeriya na soyayya da zumunci da yarda,” kamar yadda ya bayyana.

Shin za a ci gaba da karba-karba?

Sule Lamido ya ce a yanzu bayan shekara 23 bai ma kamata a dawo da maganar mulkin karba-karba ba sai dai idan da sauran rina a kaba.

“Maganar ita ce dayan biyu; ko dai har yanzu akwai wancan ciwon bai warke ba, to sai a yi shi — kama-kama — cewa har yanzu ana bukatar sulhu, wanda ke nufin ba a maganar aikin kasa ke nan sai dai maganar sulhu.

“Amma in kana maganar aikin kasa, cigaban kasa, gina kasa, inganta rayuwar mutane, zaman lafiya mu yi suna a ko’ina a duniya, kamata ya yi a ce a koma bangaren wa zai iya? wa ya dace ya yi?

“Ko Inyamuri ne ko Bahaushe ko Angas ko dan Fulani ko Kirista, shi ne a  kalli wanda zai iya din.

“Amma in ana ganin cewa har yanzu ba mu kai matsayin da za a yi maganar iyawa ba, sai maganar maganin fushi, maganin cewa sai nawa ne, ko kaza-kaza, to a je a yi ta yi!

“Amma maganar ita ce har yaushe za a ce a’a, ni nawa zan yi? Ina maganar kasar kuma?”

Yadda Najeriya ta shiga tsaka mai wuya

Da ya juya kan batun masu neman ballewa domin kafa kasashen Biyafara da kuma Jamhuriyar Oduduwa, da kuma matsalar tsaro a Najeriya, Sule Lamido ya ce duk abu daya ne ya haifar da su.

“Ko ina a Nejeriya akwai wadannan masifun, saboda haka maganar ita ce me ya kawo su? Shugabanci mara adalci.

“Idan akwai shugabancin da yake ya san hakkin mutane da ba su hakkinsu, wallahi wadannan abubuwa ba za a yi su ba,” inji shi.