✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mardia da Zainab: Mata biyu da suka fi sha’awar kallon kwallo sama da fim

Ai har yanzu ina girma ina jin abin na kara shiga raina.

Aminiya ta tattauna da wasu mata guda biyu da suka fi sha’awar kallon kwallon kafa fiye da kallon fina-finai.

A tattaunawar, wata matashiya mai suna Mardia Umar ta bayyana wa Aminiya dalilai da kuma hujjojin da suka sanya ta zabi kwallon kwallo fiye da kallon fina-finai.

Me ya sa kika zabi kallon kwallo fiye da kallon fina-finai?

Abin da ya sa na zabi kallon kwallo shi ne: Wasan kwallo yana yi wa mai kallo na ji kamar yana wajen da ake yi, fim kuwa ji yake tamkar maimaici ne.

Misali, ana iya cewa, fim din na soyayya ne ko na yara ne. Amma kallon kwallo kowa zai iya zama ya kalli wasan, misalin kallon kwallon kamar idan za a yi wasa da Najeriya, za mu iya kallon wasan a kasarmu tamkar suna yi ne muna wajen, don zai iya kara wa kasarmu daraja ta samu girmamawa daga sauran kasashe.

Kallon kwallo ba kamar fim ba ne wani ba zai iya cewa, wani abu ba zai iya faruwa ba, idan mutum yana kallon abin da ake nuna wa a zahiri yake, gaskiya ne abin da yake faruwa, kuma mutum zai rika jin dadi abin idan yana kallo a talabijin ko filin wasan kwallo.

A matsayinki na mace ta yaya kika fara kallon kwallo?

Wasu mata idan suka ga ina kallon kwallo suna dauka tamkar babu wani nishadantarwa a ciki tamkar barci zai iya daukar mutum, amma ni a bangarena abin ba haka yake ba.

Na fara kallon kwallo tun ina shekara bakwai, lokacin ina makarantar firamare, ’yan uwana a gida za su zauna su yi ta maganar kallon kwallo, misali Najeriya za ta yi wasa da Amurka ko Jamus ko wata kasar waje, abin yana ba ni mamaki idan suna labarin ’yan wasan Najeriya kamar Jay-jay Okocha ya yi wasa mai kyau ko Kanu Nwankwo.

Idan suna labarin sai na ji to me zai hana ni na yi magana kan wadannan batun.

Me ya fi ba ki sha’awa kan kallon kwallo?

Kwallon kafa abin mamaki ne, musamman idan masu sha’awar kallon na yin bayani game da wasa, kamar masu yin sharhin wasanni sun kasance masu hikima matuka yadda suke yin Turancin da kuma yadda harba kwallon a tsakanin junan ’yan wasa da kuma yadda ’yan wasa ke gudu ba sa gajiya.

Abin yana ba ni mamaki yana ba ni sha’awa kamar yadda mutum ya horar da kansa kan tunanin yadda zai zura kwallo a raga da kuma yadda zai yi tunanin tsayawa a gurbin da ya kamata don a tura masa kwallo ko suna son su zura ta a raga.

Hakan yana sani na zama kamar akwai wata baiwa da suke da ita.

A ina kike kallon kwallon kafar?

Ni a gida nake kallo kuma ina jin dadin kallon.

A yanzu kin san yadda gasar wasannin kwallon kafa ke kasancewa a duniya?

Eh tabbas na sani shirin wasanni da nake gabatarwa a tashar talabijin ta TrustTV amma ba na bayyana sunana har yau ina yi mai suna Trustsport in 60 seconds.

Na fi son kallon abin da babu wanda ya san karshensa – Zainab

A nata bangaren kuma, Zainab Nasir Ahmed wadda ’yar Jihar Kano ce, ita ma ta bayyana ra’ayinta kan sha’awar kallon kwallon kafa sama da fina-finai.

Me ya baki sha’awar kallon kwallo fiye da kallon fina-finai a matsayinki na Bahaushiya?

Gaskiya ba kasafai ake samun irin wannan ba, saboda idan an duba ai kallon kwallo ba wai kawai na maza ba ne kawai, kowa zai iya kalla kuma zai iya nishadantuwa.

Don haka ni ina sha’awar kallon kwallo sosai tun ina karama, na taso ina kallon kwallo kuma na fi jin dadin kallonsa fiye da fina-finai saboda ni, ba na son ina kallon abin da har na san abin da zai faru a karshe.

Na fi son kallon abin da yake faruwa babu wanda ya san karshensa, sai lokacin tashi ya yi an busa tashi sannan mutane za su iya yin bayanin abin da ya faru a karshe.

Wannan abin yana daga cikin abin da ya sa na fi son kallon kwallon kafa fiye da kallon fina-finai.

Kamar daga wane lokaci kika fara kallon kwallon kafa?

Na fara ne tun ina karama, saboda na taso a gidanmu ina da yayye maza da kannai muna wasan kwallon tare, idan an yi wasan kuma za a zo ana kallon kwallon ta gaske a talabijin, tun ba ma gane wa wasu suce na fi son farare wasu kuma su ce sun fi son jajaye muna amfani da launin Jessy ko kuma idan ana yin kamar ta kasashe kamar Gasar Cin Kofin Afirka da Gasar Cin Kofin Duniya da sauransu.

Daga haka ne na fara sha’awar kallon tun tasowata. Kamar ina da kungiyar wasa da nake kauna kuma har yanzu ina ci gaba da a kallonsu hakan ya sa abin ya zamar min jiki.

Don ni ba abin da nake jin dadin kallo da ya wuce kwallo. Shi kadai ne nake daukar lokaci na zauna tsawon minti 90 ina kallo, ko an kara lokaci ina zama na kalla. Amma kuma idan kallon fim ne ko minti 30 ne zan ji na kosa na tashi.

Me ya fi ba ki sha’awar kallon kwallo kafa?

Eh, na taso ne naga a gidanmu mafi yawancinmu muna kallon kwallo kuma yawancinsu maza da matan duka suna yi, don haka ba wai ni kadai ne nake kallo ba.

Kamar yadda idan ka taso da abu, tun kana yaranta za ka ji abin ka saba da shi ya zamar maka jiki ka saba da shi ya shiga ranka.

Misalin irin abin da za ka ji ya shiga cikin ranka wanda zai iya nishadantar da kai, ba kamar fim ba sun riga sun san me zai faru, za a ji wasu na cewa ai a karshen fim din wani jarumi a ciki mutuwa yake ko kuma waccar ma a karshe suna komawa su yi aure, to me ye amfanin kallonsa.

Idan kuwa kallon kwallo ce, ba wanda ya isa ya fadi wannan maganar, sai abin da hali ya yi idan an kammala kallo, wannan ne ya sa min sha’awar kallon sosai da sosai.

A cikin masu kwallon tun daga alkalai har zuwa ’yan wasa da masu kallo wanne suka fi birge ki?

’Yan wasan ne suka fi birge ni.

Kina da kungiyar kwallon kafar da kike goyon baya?

Eh, ina goyon bayan kungiyar Arsenal ce tun lokacin da na fara kallon kwallon kuma har yanzu ina goyon bayanta.

Misalin wasu ’yan wasan wasu za su zo su tafi har kocin, amma idan kana goyon bayan kungiyar ce kowa ne kake so.

Ni ba dan wasa nake yi ba, kungiyar nake yi koma wa za a kawo ya yi mana wasa, shi ne ya fi sani farin ciki kuma nasarar kungiyata nake so.

A matsayinki na mace ’yar Arewa a ina kike kallo?

Gaskiya ni a gida nake kallo, saboda ganin yadda muke sha’awar kallon kwallon kafa da ’yan uwana an hada mana tashoshin a gida.

Saboda mafi yawanci ’yan Arewa mata ba sa kallo a gidajen kallo, wani lokacin za a ji an yi rigima, wani lokacin kuma za a ga wasannin dare ne sai dare ya yi za a dawo da sauransu.

A gidanmu mahaifinmu ba ya son muna zuwa gidan kallo sai ya kasance muna cikin damuwa, sai dai idan an sa a labarai mu gani.

Da ya fuskanci wannan sai ya hada mana tashoshin da ake nuna wadannan wasannin ko ba wuta akwai janaraito.

A takaice dai a gida nake kallo, sai dai wani lokacin idan na yi tafiya na samu wajen da ba wai zallar maza ne ke kallo ba akwai mata, ina kallo.

Har yanzu kina son kallon kwallo fiye da fina-finai?

Ai har yanzu ina girma ina jin abin na kara shiga raina.

A duk lokacin da kungiyar da nake so za ta yi wasa zan sani ko da ban da lokaci zan bibiyi abin a duk inda nake, zan kalla zan duba, ina bin labarai me yake faruwa ya yi nasara wa ye bai yi nasara ba, wani lokacin a dan yi muhawara da wasu a shafukan sada zumunta na zamani.

Kina da mata ’yan uwanki masu kallon ne da kuke muhawarar?

Eh, akwai amma maza sun fi yawa wani lokacin wasu za su yi ta mamakin yadda ina mace nake son kallon kwallo, yaya ake nake ganewa da sauransu, wasu sai su ce su idan suna kallo ba su san me ake yi ba.

Wani lokacin har zama nake na yi don ko zan iya kallon fim, amma sai na ji ba zan iya ba, ba ya min dadi. Idan ba kallon kwallo ba na fi son na zauna na saurari wakoki na Hausa ko na Indiya ko Turanci, amma dai ba kallon fina-finai ba.