✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maroko ta rusa min mafarkina na lashe wa Portugal Kofin Duniya — Ronaldo

Ya ce ya yi iya bakin kokarinsa, amma hakansa bai kai ga cim ma ruwa ba

Dan wasan kasar Portugal da ya taba lashe kambun Ballon d’Or har sau biyar, Cristiano Ronaldo, ya ce duk wani mafarkin da yake da shi na lashe wa kasarsa kofin duniya ya zo karshe.

Portugal dai ta kwashi kashinta ne a hannun kasar Maroko a ci gaba da fafata wasannin a Gasar Cin Kofin Duniya da ake yi a kasar Qatar, ranar Asabar.

An ga dan wasan dai yana zubar da hawaye lokacin da yake fita daga filin wasa bayan kammala fafatawar.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, Ronaldo ya ce mafarkin nasa na lashe wa kasarsa kofin ya zo karshe.

Ya ce, “Ba ni da wani burin da ya wuce lashe wa Portugal Kofin Duniya. Na samu nasarori da kambu iri-iri, amma samun cim kofi mafi daraja a duniyar kwallon kafa ga kasata ne babban burina.

“Na yi iya bakin kokarina. A gasar har karo biyar, tsawon shekara 16, na yi aiki tukuru da sauran ’yan wasa da kuma goyon bayan miliyoyin al’ummar Portugal. Ban taba yin saduda ba daga wannan mafarkin nawa.

“Sai dai abin takaici, jiya [Asabar] wannan mafarkin ya zo karshe. Ina so ku san cewa an yi ta yamadidi da yada jita-jita iri-iri da rubuce-rubucen shifcin gizo a kaina, amma sadaukarwata ga Portugal ba ta sauya ba. Kullum mafarkina daya ne.

“Ina godiya Portugal, ina godiya Qatar. Mafarkina na yi kokarina wajen tabbatar da shi. Ina fatan yanzu kowa zai samu yanayin da zai ci gaba da fadin albarkacin bakinsa,” kamar yadda Ronaldo ya wallafa.