✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maryam Booth ta lashe Kyautar Jaruma Mace na AMAA 2020

Yadda tauraron jarumar Kannywood Maryam Booth ya haska a bikin AMAA 2020

Jarumar fim a masana’antar Kannywood, Maryam Booth ta lashe kyautar Jaruma Mace Mafi Iya Mara Baya a Kayutar Fina-finan Afirka (AMAA) na shekarar 2020.

Maryam Booth ta samu kyautar ce saboda rawar da ta taka a fim din ‘The Milkmaid’; ta doke wadda ta zo a matsayi na biyu, Chairmaine Majeri, wadda ta taka makamanciyar rawar a fim din ‘Mirage’; sai kuma Linda Ejiofor a fim din ‘4th Republic’ a matsayi na uku.

“Ina taya kaina murna da kuma iyalan fim din Milkmaid. Karin nasarori na tafe. Sai mun hadu a kyautar Oscars,” kamar yadda jarumar ta Kannywood ta wallafa a shafinta na Instagram.

Tauraro a Kannywood, Ali Nuhu na daga cikin ’yan sahun farko da suka taya Maryam murnar samun wannan kyauta ta AMAA 2020.

“Maryam Booth ’yata ina murnar wannan kyautar AMAA da kika samu bisa cancanta a matsayin Jaruma Mace Mafi Iya Mara Baya a fim din ‘The Milkmaid’Yanzu aka fara,” inji shi.

Bikin bayar da kyautar ya gudana ne ta bidiyo, a ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, 2020, wanda jarumin fim, Lorenzo Menakaya ya gabatar.

Fim din ‘The Milkmaid’, shi ne masana’antar fim din Najeriya ta gabatar domin gasar kyautar Oscars ta 2021, kuma Desmond Ovbiagele shi ne ya bayar da umarni.