✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maryam Booth ta zama jakadiyar kamfanin cingam da alawa

Fitacciyar jarumar fim din Hausa, Maryam Booth ta zama jakadiya ta farko na kamfanin alawa da cingam na Sumal da ke Kano.

Fitacciyar jarumar fim din Hausa, Maryam Booth ta zama jakadiya ta farko na kamfanin alawa da cingam na Sumal da ke Kano. 

Kamfanin abinci na Sumal Foods Limited ya kaddamar da jarumar ce bayan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Manajan kasuwanci na Sumal Foods, Mista Sanjay Sing, ya ce kamfanin ya zabi jarumar ne saboda ficenta da kuma yadda ta amfanar da miliyoyin mutane.

A cewarsa ayyukan da Maryam Booth ta yi ba wai kawai suna suka sa ta yi a duniya ba, ta kuma samu lambobin yabo masu yawa, ciki har da na mataimakiyar jaruma ta Africa Movie Academy Awards ta shekarar 2020.

Mista Sanjay Sing ya ce Kamfanin Yale wanda ya shafe shekaru 40 yana gudanar da ayyukansa ya yi fice wajen samar da kayayyakin abinci da suka hada da biskit da cingam da burodi da alawa da ke gamsar da al’ummar Jihar Kano da Najeriya gaba daya.

Ya ce, “A shirye muke mu ci gaba da samar wa al’umma ingantattun kayayyakinmu masu lafiya da sanya annashuwa.”

Da take sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar, Maryam Booth, ta bayyana shirinta na yin duk mai yiyuwa wajen bunkasa kasuwancin kayayyakin kamfanin.

“Na sani cewa nauyi ne a kaina wajen ganin na yi duk abin da ya kamata wajen ganin kowane gida na amfani da kayayyakin Kamfanin Sumal,” in ji ta.