✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maryam Laushi: Damuwa da yadda za a dama da matasa

Maryam Laushi ta yi fafutukar ganin an rage shekarun masu son tsayawa takara

Maryam Laushi matashiya ce wadda ta yi fice wajen fafutukar ganin ana damawa da matasa a al’amuran siyasa da tattalin arziki da sauran sassan rayuwa.

Tana cikin matasan da suka fara yekuwar “Not Too Young To Run” suna kira da a rage mafi karancin shekarun da doka ta yanke don tsayawa Takara.

Manufar hakan ita ce bai wa matasa dama su ma su shiga a dama da su a harkar mulkin kasa.

Tana aikin sa-kai da kungiyoyin farar hula da dama, ciki har da kungiyar matasa ta Youth Initiative for Advocacy, Growth and Advancement (YIAGA).

A shekarar 2017 Maryam Laushi na cikin matasan da aka karrama a matsayin ’yan kasa da shekara 25 da suka yi rawar gani su 25.

Shugaba mai hazaka

Da shekara ta zagayo kuma aka bai wa Tauraruwar tamu lambar yabo ta Shugabanni Masu Hazaka ’yan kasa da shekara 30 a bangaren siyasa da jagorancin al’umma.

Sannan a 2019 ta samu shiga dandalin Deutsche Welle Global Media Forum, inda kwararrun ’yan jarida da masu fada-a-ji a harkar siyasa da kungiyoyin farar hula da ilimi da kasuwanci daga sassan duniya daban-daban ke haduwa don kara wa juna sani game da yadda za a magance wadansu matsaloli.

Ta sha shiga wannan zaure don tattauna batutuwan da suka shafi zamantakewa da siyasa.

Tauraruwar tamu tana kuma taka rawa wajen yaki da cin zarafin mata a Najeriya.

Mahanga

Maryam Laushi ta yi amanna cewa Najeriya tana da kyakkyawar makoma kuma mata da matasa suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen gina wa kasar makoma ta-gari.

Tana cikin matasan da muryoyinsu ke yin tambari a Najeriya wajen tabbatar da daidaiton jinsi da adalci a tsakanin al’umma da kuma damawa da matasa a al’amuran siyasa.

A yanzu haka, Tauraruwar tana jagorantar wani kamfani mai ba da shawara a kan al’amuran yada labarai, sannan kuma tana aiki da kungiyar Save The Children mai kare hakkokin yara a matsayin Kwararriya a Bangaren Sadarwa.