Masar da Senegal sun kai matakin Semi-Final a gasar AFCON | Aminiya

Masar da Senegal sun kai matakin Semi-Final a gasar AFCON

Mohammed Salah a lokacin da yake murnar kwallon da ya ci a wasan Masar da Morocco
Mohammed Salah a lokacin da yake murnar kwallon da ya ci a wasan Masar da Morocco
    Ishaq Isma’il Musa

Masar ta kora Morocco gida a matakin daf da kusa da na karshe a gasar Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON wadda Kamaru ke karbar bakwanci.

Dan wasan kungiyar Liverpool, Mohamed Salah ne ya ci wa Masar kwallo daya sannan ya taimaka aka ci ta biyu.

Sai dai tun da farko dai Sofiane Boufal ne ya ci wa Morocco bayan ya samu bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A halin yanzu dai Masar za ta buga wasan kusa da na karshe da Kamaru mai masaukin baki a ranar Alhamis.

A daya bangaren kuma, abokin wasan Salah a kungiyar Liverpool, Sadio Mane ne ya taimaka wa Famara Diedhiou da kwallo ta farko da tawagar Senagel ta jefa a wasan da suka fafata da Equatorial Guinea, wacce ta farke ta hannun Jannck Bulya ana dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sai dai ’yan wasan da suka shigo daga baya a matsayin canji, Cheikhou Kouyate da Ismaila Sarr, kowannensu ya jefa kwallo daya.

A ranar Laraba ce Senegal za ta yi karon batta da tawagar Burkina Faso a filin wasan na Ahmadou Ahidjo da ke Doula, babban birnin Kamaru.