✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masar ta kulle masallaci saboda karya dokokin kariyar COVID-19

Ministan Harkokin Addini na Kasar Masar, Mohammed Gomaa ya bayar da umarnin rufe wani masallaci a birnin Cairo na kasar saboda karya dokokin kariya COVID-19.…

Ministan Harkokin Addini na Kasar Masar, Mohammed Gomaa ya bayar da umarnin rufe wani masallaci a birnin Cairo na kasar saboda karya dokokin kariya COVID-19.

Ministan ya ce masallacin zai kasance a rufe ne tsawon makonni biyu saboda karya dokokin kariya daga cutar da aka gindaya wa wuraren ibadar kasar.

Sashen watsa labarai na ma’aikatar ne ya tabbatar da umarnin  a wata sanrwa da ya fitar ranar Talata.

“Minista Mohammed Gomaa, bayan gudanar da sallah a masallacin Al-Nour dake yankin Abbassia, ya bayar da umarnin rufe shi na tsawon makonni biyu farawa daga ranar Talata, saboda masu ibada a cikinsa ba sa bin umarnin ma’aikatar na yin amfani da takunkumin rufe fuska da kuma na zuwa da daddumar yin salla ga kowanne mai yin sallah,” inji sanarwar.

Kazalika, ma’aikatar ta ce dukkan masallacin da ya gaza aiwatar da matakan kariya daga cutar kamar su bayar da tazara to ba za ta yi wata-wata ba wurin rufe shi.

A ranar 27 ga watan Yuni ne Masar ta sanar da sake bude masallatai bayan kawo karshen zagayen farko na annobar Korona a kasar.

A karshen watan Agusta ne kuma aka amince a dawo da yin sallar Juma’a, bisa sharadin bude masallaci mintuna 10 kacal kafin lokacin tayar da sallah, a rufe shi da zarar an idar, da kuma takaita huduba zuwa mintuna 10.

Har ila yau, har yanzu haramcin da aka saka na hana taruwa yayin gudanar da jana’iza a kasar na nan daram.

Ma’aikatar Lafiya ta kasar dai ta sanar da sake barkewar annobar a karo na biyu ranar 23 ga watan Nuwamban 2020.

A cewar ma’aikatar, sama da mutane 133,000 ne suka kamu da cutar a fadin kasar, yayin da sama da 110,000 kuma suka warke.

Adadin wadanda suka mutu kuma sanadiyyar cutar a kasar ya kai 7,466.