✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Rano ta dakatar da dagattai kan ‘satar tallafin COVID-19’

Masarautar Rano da ke jihar Kano ta dakatar da wasu Dagattai bisa zarginsu da aikata halin bera a kan kayan tallafin COVID-19.

Masarautar Rano da ke jihar Kano ta dakatar da wasu Dagattai bisa zarginsu da aikata halin bera a kan kayan tallafin COVID-19 da gwamnati ta bayar don rabawa talakawa.

Dagatan da aka dakatar dai sun hada da Dagacin garin Zurgu, Umar Yusuf da na garin Zambur mai suna Kamilu Zambur.

Sarkin Rano, Alhaji Kabir Muhammadu Inuwa ne ya ba da umarnin dakatarwar ta hannun Chiroman masarautar Rano kuma hakimin Rano Manniru Abubakar ila, umarnin dakatar da Dagatan biyu

Tuni dai masarautar ta Rano ta aike da wakilci zuwa yankunan dagatan biyu domin maye gurbin wadanda aka dakatar din.

Waiwaye kan rabon tallafin Corona a Kano

Jihar Kano na daya daba cikin jihohin da aka yi nasarar cafke mutanen da ake zargi da kalmashe kayan tallafin COVID-19 da wasu suka yi kwana da su zuwa gidadjensu ko wuraren sayarwa.

Ko a kwanakin baya an samu rahoton tuhumar da Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yakar Rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado ke yi wa shugaban Karamar hukumar Kumbotso mai ci, Hon. Kabiru Ado Panshekara bisa zargin karkatar da kayan tallafin na COVID-19.

Kazalika, cikin kasa da makonni biyu, da suka gabata, sai da Hukumar Hisba ta jihar ta dakatar da Kwamandanta na reshen karamar hukumar Dala Ustaz Siyudi Hassan, shi ma bisa zargin sama da fadi da kayan tallafin.

Hakan dai ya biyo bayan korafi da wasu ma’aikatan hukumar a karamar hukumar suka gabatar wa shalkwatar hukumar ta jiha wanda ya kai ga dakatar da Suyudi din daga mukaminsa.