✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Saudiyya ta hana Muhammad bn Salman baluguro mai nisa

Likitocin sun hana Yarima mai jiran gadon yin tafiya mai nisa a jirgi ne.

Tawagar likitocin Yarima mai jiran gadon Saudiyya, Muhammad bn Salman, sun shawarce shi da ya tsahirta da yin duk wata doguwar tafiya a jirgi saboda kauce wa matsalar kunne da doguwar tafiya a jirgi ke haddasawa.

Hakan na zuwa ne bayan da mahaifinsa Sarki Salman ya umarce shi da ya jagoranci tawagar kasar zuwa taron Kolin Kasashen Larabawa da Aljeriya ke karbar babunci.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa, likitocin masarautar ne suka fitar da sanarwar da kuma shawara ga Yariman ya dakatar da yin balaguron.

A don haka Sarki Salman ya umarci Ministan Harkokin Waje, Yarima Faisal bin Farhan, ya wakilci kasar a madadin Yarima Muhammad.

Likitocin sun hana Yarima mai jiran gadon yin tafiya mai nisa a jirgi ne, “matukar ba za a tsaya wata kasa a huta ba, domin kaucewa matsalar kunne da doguwar tafiya a jirgi ke haddasawa, sakamakon tafiyar zuwa da dawowa ta kai tsawon awa 24.”

Sarki Salman ya ce, kasar Saudiya na tare da Aljeriya a kowanne hali, tare da nanata goyon baya ga duk matsayar da za a cimma a taron kolin kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ranar 1 zuwa 2 ga watan Nuwamba za a fara taron wanda kasashe 31 na yankin Gabas ta Tsakiya za su halarta.