✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An hana Tashe a Katsina saboda dalilan tsaro

Masari ya ba da umarnin kama masu gudanar da tashe, saboda dalilan tsaro

Gwamnatin Katsina ta haramta gudanar da tashe a fadin Jihar a cikin watan Ramadan.

Kwamishinan Yada Labarna Jihar, Abdulkarin Yayaha Sirika ya ce haramcin ya shafi kowane nau’i na tashe kuma Gwamnatin Jihar ta umarci jami’an tsaro su kama duk wanda ya karya dokar.

Sanarwar da ya fitar a ranar Talata ta ce, “Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin ne saboda wasu rahotannin tsaro da aka samu.”

Ya ce, “Don haka ake jan hankali iyaye da daukacin al’umma da su sa ido a kan ’ya’yansu, sannan su haka da guji gudanar da al’adar ta tashe a fadin Jihar.

“Ya kuma umarci hukumoin tsaro da su tsare duk wanda aka samu ya saba wannan umarni.”