✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masari ya raba tallafi ga mutanen da harin ’yan bindiga ya shafa a Safana

Gwamnan ya raba kayan tallafi don rage musu radadin hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya raba kayan abinci ga mutanen da hare-haren ’yan bindiga suka shafa a Karamar Hukumar Safana ta jihar.

Kayayyakin da darajarsu ya kai sama da Naira miliyan 21 da suka hada da kayan abinci da sabulun wanka da dai sauransu, an raba su ne ga iyalai da ke yankuna biyar a karamar hukumar — Zakkah, Sabon Garin Gamji, Kunamawa, Kukar Rabo da Tsaskiya.

Kimanin mako biyu da suka gabata ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki a Karamar Hukumar Safana, inda suka kashe mutane da dama ciki har da babban jami’in dan sanda na yankin Dutsinma, ACP Aminu Umar.

A yayin rabon, Gwamna Masari, wanda ya samu wakilcin Shugaban Karamar Hukumar Safana, Muhammad Kabir Umar, ya jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu.

Gwamnan ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kayan agajin tare da yin addu’ar Allah Ya dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar da ma kasa baki daya.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da iyalan wadanda suka mutu da na wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su da wadanda suka samu raunuka sakamakon harin, da kuma wadanda aka sace musu shanu.

Sauran sun hada da wadanda suka rasa rayukansu da kuma wasu mutane tara da ke karbar magani a Cibiyar Lafiya ta Tarayya sakamakon kuskuren bam din da jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya jefa a kauyen Kunkunna.