✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masoyan El-Rufai na zanga-zanga a Kaduna

Masu zanga-zangar na goyon bayan sallamar ma'aikatan da El-Rufai ya yi.

Masu goyon bayan sallamar dubban ma’aikata da Gwaman Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi sun gunadar da zanga-zangar nuna amincewarsu da matakin da ya dauka.

A safiyar Laraba matasan suka fito dauke da kwalayen da ke yabon El-Rufai tare da sukar ’yan kwadago da ke yajin aikin gargadi kan sallamar ma’aikatan da ya yi.

Sun yi tattakin goyon bayan gwamnan ne sa’o’i kadan bayan ’yan sanda sun tarwatsa gungun wasu ’yan daba da suka mamaye ofishin Kungiyar Kwadago ta Kasa reshen Jihar.

Ga wasu hotunan masu tattakin:

Masu zanga-zangar adawa da yajin aikin kungiyar kwadago sun yi tattaki a kan Titin Ali Akilu da ke garin Kaduna. (Hoto: Mohammed Ibrahim Yaba).
Magoya bayan El-Rufai sun yi ta daga kwalayen yabon gwamnan a yayin da suke tattaki a garin Kaduna. (Hoto: Mohammed Ibrahim Yaba).
Mata na daga cikin wadanda suka fito tattakin adawa da yajin aikin da kungiyar kwadagon ta ke yi kan sallamar ma’aikata da gwmanan ya yi. (Hoto: Mohammed Ibrahim Yaba).
Magoya bayan na El-Rufai sun yi ta daga kwalaye da ke dauke da kalaman sukar ‘yan kwadago. (Hoto: Mohammed Ibrahim Yaba).
Wasu daga cikin masu tattakin adawa da yajin aikin kwana biyar da kungiyar kwadago ke yi a Jihar Kaduna. (Hoto: Mohammed Ibrahim Yaba).