✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu fasa-kwaurin shinkafa sun bude wa kwastam wuta

Jami'an kwastam da soja na karbar magani a asibiti bayan harin.

Akalla jami’an kwastam uku da soja daya ne suka ji munanan raunuka bayan masu fasa-kwaurin shinkafa sun bude musu wuta.

Kakakin Hukumar Kwastam Shiyya ta Daya, Theophilus Duniya, ya sanar da manema labarai a birnin Ibadan cewa lamarin ya faru ne a yankin  Igboora na Karamar Hukumar Ibarapa ta Jihar Oyo.

“Jami’an kwastam da ke aiki sun hangi tirela takwas dauke da shinkafar da aka yi fasa-kwaurinta, amma nan take direbobin motocin suka farmake su.

“An harbe daya daga cikin wadanda suka farmaki jami’an tsaron an kuma kwace makaminsa, ragowar kuma sun tsere.

“Ana ci gaba da binciken wadanda suka kai harin don gurfanar da su a gaban kuliya, dukkannin jami’an da suka ji rauni, ciki har da soja daya  kuma suna samun kulawa,” a cewar Duniya.

Ya ce DC Usman Yahaya, ya yi Allah wadai da harin, tare da ba da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yakar masu fasa-kwaurin shinkafa a fadin Najeriya.

A cewarsa, daukar makamai da wasu bata-gari ke yi ba zai hana jami’an hukumar yin aikinsu ko yakar masu fasa-kwaurin shinkafa ba.