Masu garkuwa da mutane 13 sun shiga hannu a Adamawa | Aminiya

Masu garkuwa da mutane 13 sun shiga hannu a Adamawa

Jami’an ‘Yan sanda
Jami’an ‘Yan sanda
    Amina Abdullahi, Yola da Sagir Kano Saleh

’Yan sanda sun kama wasu mtum 13 da ke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a Jihar Adamawa.

Dubun masu garkuwa da mutanen ta cika ne bayan ’yan sanda sai kai samame a maboyar bata-garin inda suka kwato bindigogi biyar da sarkar daure mutanen da suka sace.

Da yake gabatar da bata-garin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, SK Akande, ya kara da cewa an kwace kayan sojoji da tsabar kudi N358,500 daga hannunsu.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce an yi wa masu garkuwa a mutanen dirar mikiya a maboyarsu ne bayan samun bayanan sirri.

Ya kara da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen farauta da kuma kamo sauran bata-garin da suka tsere.