✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da mutane bayan sun kashe mutum 18 a masallaci na neman N18m

Hakan na zuwa ne bayan sun kashe mutum 18 yayin harin.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masallata a kauyen Maza-Kuka da ke Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja bayan sun kashe mutum 18 sun bukaci a basu Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa.

A ranar Litinin ne dai maharan suka yi wa garin kawanya sannan suka bude wa mutane wuta suna tsaka da sallar Asuba.

Wata majiya daga yankin, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa an sace mutum 11, ciki har da limamin masallacin.

“Sun kira waya jiya, suna neman a biya su Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa.

“Yanzu dai gaskiya ba mu san yadda za mu yi ba. Ko da yake masallacin na Juma’a ne, amma limaminsa na daga cikin wadanda aka sace, tare da wasu mutum 10,” inji majiyar.

Aminiya ta gano cewar daga cikin wadanda aka kashe yayin harin har da wata mace.

A cewar wani wanda ya ce matar abokinsa ce, ya ce, “Lokacin da suke kai harin, sai ta kwalla ihu sannan ta yi kokarin guduwa, shi ya sa suka harbe ta, ta mutu nan take.

“In da ba don ihun da ta yi ba, da ba za su kashe ta ba. Ba su kashe ko sace ko da mace daya ba.”