✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun bukaci Sigari da Tabar Wiwi a matsayin fansa

Tuni dai aka kai musu kamar yadda suka bukata, kuma har sun sako mutanen.

’Yan bindigar da suke addabar wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja sun tilasta wa mutanen yankin kai musu kwalayen sigari da kullin tabar wiwi a matsayin fansar ’yan uwansu da suka yi garkuwa da su.

Aminiya ta rawaito cewar akwai mutane da dama daga yankin Zazzaga da Cibani da ma wasu a yankunan da suka shafe kusan mako biyu a hannun masu garkuwar.

Wani mamba a kwamitin tsaro na yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa sai da aka kai wa ’yan bindigar kwayoyin ranar Talata kafin su sako wasu ’yan yankin.

Ya ce, “An yi garkuwa da ’yan uwanka, duka abin da ka san zaka iya yi wajen kubutar da su dole ne ka yi.

“Daga ciki akwai wasu yara da aka sace a daya daga cikin irin wadannan hare-haren a gona. Tuni iyalan suka kai musu kayan da suka bukata, kuma har sun sako wasu daga cikinsu,” inji shi.

Ya kuma ce masu garkuwar sun bukaci a ba su garin masara da fakitin kafi-zabo da jarkar man fetur guda biyar, kuma tuni an kai musu.