✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da Sarkin Kajuru na neman N200m a matsayin kudin fansa

Daya daga cikin masu rike da sarauta a masarautar ne ya tabbatar da hakan.

Masu garkuwa da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna sun bukaci a ba su Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa.

An dai yi garkuwa da sarkin ne da wasu iyalansa su 12 a fadarsa da ke garin na Kajuru a da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Daya daga cikin masu rike da sarauta a masarautar ne ya tabbatarwa da Aminiya cewa masu garkuwar sun tuntube su ta waya suna neman a basu N200m.

Muna tafe da karin bayani….