✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudin fansa: Masu garkuwa da ‘Uwar Marayu’ na neman N100m

“Sai dai a taya mu da addu'a domin ba mu san ta ina za mu fara hada Naira miliyan 100 ba,” inji wani makusancinta

Wadanda su kayi garkuwa da tsohuwar malama a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna, Dakta Rahmatu Abarshi sun bukaci Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansarta da sauran wadanda aka kama su tare su uku.

An yi garkuwa da Hajiya Abarshi ne ranar Juma’a da yamma a kan hanyar Kachia zuwa Kaduna bayan sun dawo rabon kayan tallafi ga wasu marayu a yankin Mariri da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

“Sai dai a taya mu da addu’a domin ba mu san ta ina za mu fara hada Naira miliyan 100 ba,” inji wani makusancinta, Abdallah Isma’il Abdallah.

Abdallah, wanda suke tare a motar kafin abin ya faru da ita, ya ce sun je kauyen Tilden Kargiji ne a Karamar Hukumar Lere inda ta dauki nauyin raba wa marayu 40 tufafi yadda ta saba yi a karkashin kungiyarta ta Barkindo Rahama Initiative, kafin kaddara ta faru da su a kan hanyar komawa gida.

“Da yake ba rabon abin ya faru dani, ni na sauka don zuwa Ladduga wajen ’yan uwanmu sai dai labari kawai muka ji cewa masu garkuwa sun tare motar da suke ciki sun yi awon gaba da abokan tafiyarta su uku,” inji shi da yake yi wa Aminiya karin haske.

Ya ce zuwa yanzu suna kan tattaunawa da masu garkuwan inda suka bukaci a ba su Naira miliyan 100.