✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa sun koma karbar kudin fansa ta banki a Abuja

"Ana wasa wuka za a yanka ni sakon kudin ya shigo wayar masu garkuwar."

Masu garkuwa da mutane a Abuja sun kara tsaurin ido inda suka fara karbar kudin fansar mutanen suka sace ta banki, sabanin yadda a baya suke karbar tsabar kudi.

Bincikenmu ya gano yadda wasu mutane suka biya ’yan bidiga kudin fansa ta banki kafin su sako ’yan uwansu da suka yi garkuwa da su.

Wata matar da aka yi garkuwa da ita ta bayyana wa wakilinmu yadda ’yan bindigar suka kekashe kasa cewa dole a biya su kudin fansa ta banki, ba sa son tsabar kudi.

Ta ce har masu garkuwar sun fara wasa suka ga za su yanka ta saboda an yi jinkiri, sai suka ji shigowar sakon kudin da aka tura musu ta banki.

A makon jiya kadai, ’yan bindiga sun yi kwana biyu a jere suna kai hari tare da sace mutane a Tungan Maje da ke wajen birnin Abuja, inda suka dauke mutum shida ranar Talata, ranar Laraba kuma suka sake dawowa suka dauke wasu.

A cikin ’yan watannin nan, an sami karuwar garkuwa da mutane a yankunan da ke kewayen birnin Abuja kamar Kuje, Bwari da Abaji da sauransu.

A baya masu garkuwar na sakin mutanen da suka sace bayan sun karbi fansa a tsabar kudi, amma yanzu da alama suna karbar kudaden fansar ta banki.

‘Yadda masu garkuwa suka sa mu biya su ta banki’

Wata matar auren da aka yi garkuwa da ita ta bayyyana wa wakilinmu yadda masu garkuwar suka tursasa mijinta ya biya kudin fansarta ta banki kafin su sako ta.

Mijin matar ya nuna wa wakilinmu takardar banki ta shaidar biyan kudin da ya tura wa masu garkuwar.

Ta ce a ranar Laraba, 16 ga Yuni ne aka yi garkuwa da ita tare da wasu fasinjoji mata hudu a Mahadar Madalla, a hanyarsu ta zuwa sayayya a Kasuwar Ibrahim Babangida da ke Suleja, Jihar Neja.

Matar ta kuma tabbatar mana da cewa dangin sauran ​​wadanda aka sace su tare sun biya kudin fansa tsakanin N500,000 zuwa N1,000,000 zuwa wani asusun banki da ’yan bindigar suka bayar kafin su sako su.

Wani dan uwanta ya ce Naira miliyan biyar masu garkuwar suka fara nema a kan kowane mutum daya, bayan kwana biyu ana tattaunawa da su ana rokonsu kuma suka amince da karbar N500,000 daga danginta.

Ya ce ’yan bindigar sun yi barazanar yanka ta idan ba a biya kudin cikin sa’a 48 ba, suka kuma nace cewa ta banki za a tura musu kudin ba tsabar kudi ba.

Takardar biyan kudin fansa, wacce Aminiya ta samu kwafinta ta nuna cewa mijin matar ya biya N500,000 a cikin wani asusun bankin Access mai lamba 1403762272 da sunan Badawi Abba Enterprise.

Yadda motar fasinja ta yi garkuwa da mu

Da take bayyana yadda abin ya faru matar ta ce, “Mun hau motar bas a mahadar da ke kusa da gidan mai na SARCO, daura da Mahadar NYSC da ke Kubwa, za mu je Kasuwar Suleja.

“Yawancin fasinjojin motar sun sauka ne a Zuba, saboda haka direban ya so ya sauke sauran fasinjojin amma ya karasa da mu zuwa Mahadar Madalla — hanyar da ke zuwa Dakwa.

“Da muka isa Mahadar Madalla, sai ya ce sai dai mu nemi wata motar zuwa Suleja. Sai mu biyar (mata) da muka rage muka tsayar da wata mota da ke kiran “Suleja! Suleja!!” kuma direban bas din namu ya yi masa juyenmu, muka tafi.

“Shigarmu motar ke da wuya sai direban ya kulle duka kofofinta ya daga gilasai, a lokacin ne muka san cewa duk gilasan masu duhu ne.

“Mu hudu ne ke zaune a kujerar baya, wasu mutum biyu kuma suna a gaba tare da direban.

“Suna gama daga gilashin, sai suka fito da bindigogi da wukake da kwalaban Coca-Cola, cewa mu ba da hadin kai, suka ce mu sha lemon da suka surka da Kodin amma na ni na ki.

“Mutumin da ke gaba ya daga wuka, ya ba ni Kodin kadai in sha, amma sai na yi kamar na kurba. Bai iya yi min komai da wukar ba saboda motar ta matse shi.

“Wasu daga cikinmu da suka sha Coke din har sun fara barci kafin a isa dajin da aka kai mu.

“Duk da cewa ban yi barci ba, ba zan iya gane inda suka kai mu ba. Na dai san cewa motar da ta kawo mu ta juya ne bayan Kwata a gaban Suleja — Kana wuce Kwankwashe sai Kwata.

“Motar ta shiga cikin daji da mu, da aka kai inda ba za ta iya ci gaba da tafiya ba, sai muka tarar da wasu mutum uku suna jira da babura, suka dauke mu a baburan zuwa cikin kungurmin daji.

“Gida daya ne kawai a cikin dajin. A can aka tsare mu, babu abun da suke ba mu sai burodi da ruwan leda.

“A ranar da muka je aka saki daya daga cikinmu saboda tana da kudi a cikin asusun ta na banki ta kuma tura musu kai tsaye bayan mun isa wurin.

“Bayan kwana biyu, har sun fara wasa wukakensu za su yanka ni saboda ba su samu sakon kudin daga mijina ba, Allah Ya cece ni a ranar,” inji ta.

An sanar da ’yan sanda 

Mijin matar ya shaida wa wakilinmu cewa a lokacin, ya gabatar da rahoto a hukumance a sashin yaki da satar mutane na ’yan sanda da ke Jabi a Abuja.

Mun tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda da ke Abuja, ASP Mariam Yusuf, ta kuma tabbatar mana da cewa Rundunar tana amfani da dabaru na boye da na fili don gano masu aikata laifuka da suka hada da masu satar mutane a Birnin Tarayya.

‘Gano masu garkuwa da banki abu ne mai sauki’

A watan Afrilu, tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Kingsley Moghalu, ya yi zargin cewa ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane sun fara neman a biya su fansa ta hanyar kudaden Cryptocurrency.

Duk da cewa bai fayyace miyagun da ya ce suna amfani da hanyar ba, amma ya ce hakan na bukatar a tsaurara matakan kulawa a kan kasuwar Cryptocurrency a duk duniya.

Wasu ’yan Najeriya sun koka kan yadda bankuna suke kawo musu cikas wajen samar da bayanan masu aikata laifuka ta hanyar amfani da asusun banki.

Hamisu Ibrahim, wani mazaunin Abuja ne, ya ce tsare-tsaren banki sun sa shi asarar kudadensa da wasu masu damfara suka sa ya biya ta banki.

Wani masani kan damfara ta kudi, Umar Yakubu, ya ce gano masu aikata laifuka da ke amfani da banki abu ne mai sauki, sai dai idan ba a ga dama ba.

Gano masu gakuwa ya zama siyasa — Masani

Wani masanin laifuffukan kudi kuma tsohon ma’aikacin Hukumar EFCC, Umar Yakubu, ya ce halin da ake ciki da har masu garkuwa suke neman karbar kudin fansa ta banki ya nuna cewa ganowa masu laifi ya zama zabi na siyasa.

Yakubu, wanda kuma shi ne Shugaban cibiyar yaki da rashawa ta Counter Fraud Centre, ya shaida wa wakilinmu a hirarsu ta wayar tarho, cewa muddin aka ci gaba da yin hakan, to ba za a kawo karshen matsalar ba kuma za ta ci gaba da yin illa ga tattalin arzikin kasa.

Ya ce, “A duk al’amuran da suka shafi aikata laifi kowane iri, akwai kokarin hana a gano masu aikatawa. Shi ya sa ake kafa hukumomin da ke tabbatar da doka — don su yi bincike su gano masu aikata laifi.

“Amma yadda muke a yanzu wanda har masu aikata laifi suke neman a biya su kudin fansa ta hanyar cibiyoyin hada-hadar kudi, wadanda kuma suke da bayanan duk kwastomominsu, to abin tsoro ne, domin ya nuna ba sa tsoron a gano su ke nan.

“Don haka, ba sai an bata lokaci ba za a gano ko su wane ne. Ya kamata a san su. Kada gwamnati ta sake ta bude kofar da zai sa ta yi nadama.

“Misalai a Mexico, Iraki, Afghanistan, Indiya da sauran kasashe da ke fama da matsalar satar mutane don neman kudin fansa, ba a taba samun an biyan kudi ta asusun banki ba.

“Gwamnati na bukatar sake tunani saboda idan ba ta magance wannan matsalar ba, to za ta bude kafar karuwar masu aikata irin wadannan laifuka.

‘Abin da gwamnati ke yi’

Mun tuntubi jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN) amma ba su ba da amsa a hukumance ba kan tambayoyin da muka yi musu game da abin da gwamnati ke yi domin magance matsalar.

Amma wata majiya daga hukumar gudanawar CBN ta ce: “Abin da bankunan kasuwanci za su iya yi shi ne kawai su rufe asusun ajiya duk wanda EFCC ko hukumar ’yan sanda suka bukata bisa umarnin kotu.

“A ko da yaushe, CBN da bankunan kasuwanci na ba da hadin kai ga hukumomi ta hanyar ba su sahihan bayanai a kan huldodin da ba a aminta da su ba, kuma hakan na kaiwa ga tsare masu laifi, daidai da bukatar sashen bin diddigin kudade (NFIU).

“A yanzu dole bankuna su sanya ido kan kudaden da ke gudana ta hanyarsu, tare da sanar da hukumomi duk abin da suke bukatar sani — misali, tura kudade zuwa wata kasa mai hatsarin gaske wanda bai dace da tarihin kwastomomi ba — don taimakawa gano kudaden haram, ba da kudaden ’yan ta’adda ko wasu laifuka.”

NFIU ita ce cibiyar kasa da ke da alhakin karbar bayanai daga hukumomi masu samar da rahoto, sannan ya yi nazarin bayanan da kuma samar da su ga hukumomin da suka dace domin su yi aiki a kansu.

NFIU sashi ne mai cin gashin kansa a CBN kuma ita ce babbar cibiyar yaki da hada-hadar kudade ta haramtacciyar hanya ta kasa, taimaka wa ’yan ta’adda da dangoginsu.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kakakin NFIU, Sani Tukur, amma ya tura shi ga jami’an tsaro, yana mai cewa NFIU ba ta bincika ko kama wadanda ake zargi.

Amma wani babban jami’i wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce hukumar tana aiki da bayanan sirri na kudi kan masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga wadanda take mika su ga jami’an tsaro don daukar mataki.

Ya ce yanzu hankalin NFIU zai koma kan ’yan bindiga da masu garkwua da mutane saboda a cewarsa, sun riga sun tsinka lakar bakin Boko Haram da dangoginta ta fuskar su ta hanyar kudi.

Dokar haramta biyan kudin fansa

Majalisar Tarayya na ci gaba da aiki kan kudurin dokar haramta biya ko karbar fansa don sakin mutanen da aka sace, ko aka tsare ba da son ransu ba.

A ranar 19 ga watan Mayun 2021, Majalisar Dattawa ta amince da kudirin Dokar Hana Ta’addanci ta 2021, don karatu na biyu yayin zamanta.

Da yake gabatar da kudurin, Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ya ce dokar na neman maye gurbin sashi na 14 na Babbar Dokar kuma gabatar da wani sabon sashi.

Gyaran shi ne: “Duk wanda ya tura kudade, ya biya ko ya hada baki da wani mai satar mutane ko dan ta’adda don karbar duk wani fansa don sakin wanda aka tsare shi ba bisa ka’ida ba, aka daure shi ko aka sace shi, to ya aikata babban laifi da za a yanke masa hukuncin daurin shekar 15 a gidan yari.”

Da yake danganta yawaitar sace-sacen mutane ga rashawa, rashin aikin yi, talauci da hadin bakin jami’an tsaro, dan Majalisar ya koka cewar matsalar tafi sauran nau’ukan laifi kamari tare da jefa akasarin ’yan Najeriya cikin hadari.

Ya ambato wani rahoton da jaridar Financial Times da USA Global Risk Consultancy suka wallafa a watan Nuwamban 2019, cewa Najeriya ce kan gaba wajen yawan sace-sacen mutane don neman kudin fansa  a Afirka.

A cewarsa, “Dalilin da ya sa ake biyan kudin fansa ya samo asali ne daga yadda mutane ke iya fahimtar wahalar mutumin da aka yi garkuwa da shi.

“Duk da haka, tarihi ya nuna cewa ko da an biya fansa, ba za a lamunce da ran ko dawo da wanda aka sace ba lafiya.”

Ya lura cewa kasashe kamar Amurka da Ingila basa goyon bayan biyan kudin fansa ga masu satar mutane.