✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu gurasa za su shiga yajin aiki sai abin da hali ya yi a Kano

Sun ce dole kamfanoni su rage farashin fulawa ko kuma su fara yajin aiki.

Kungiyar Masu Gurasa ta Jihar Kano ta yi barazanar shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a fadin Jihar, matukar kamfanonin fulawa na BUA da IRS da Golden da Super ba su dawo da farashin fulawa zuwa Naira 9,000 ba.

Masu gurasar sun yi barazanar ce a wata takardar da suka fitar mai dauke da sa hannun Shugabar Kungiyar, Fatima Auwalu, wacce aka raba wa manema labarai.

“’Ya’yan kungiyarmu suna yin gurasa ne da fulawar BUA da Golden da IRS da kuma Super. Amma kaf dinsu babu wacce farashinta bai tashi ba,” inji Shugabar kungiyar wadda ta yi kira ga masu kamfanonin fulawar da su rage farashin tun kafin abubuwa su lalace.

Ta ce, a baya suna sayen fulawa ne kan Naira 9,500 amma yanzu kudin ya tashi zuwa Naira 16,200.

“So muke yi kamfanonin fulawa su mayar da farashin zuwa Naira 9,000 ko kuma mu daina yin gurasar gaba daya,” kamar yadda ta ce.

‘Ba mu kadai za ta shafa ba’

Ta kara da cewa, “Ina amfani da wannan dama wurin yin kira ga Abdussamad Isyaka Rabiu da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta rage farashin fulawa ko kuma mu hakura da sana’ar yin gurasa.

“Idan muka dakatar da yin sana’ar ba mu kadai abin zai shafa ba, zai shafi sauran al’ummar wannan jiha tamu da ma sauran al’ummu a fadin Arewa,” inji ta.

Wata mai sana’ar gurasa, Usaina Adamu ta bayyanawa manema labarai cewa, dole ce ta sa za su shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani, saboda yajin aikin gargadi na kwana uku da suka yi bai cimma biyan bukata ba.

Ta ce: “Fatarmu ita ne masu ruwa da tsaki, musamman gwamnati za ta shigo cikin wannan lamari, don ganin an sauko da farashin fulawa.

“Haka nan kuma ina kira ga Abdussamad Isyaka Rabiu da kamfanin IRS, Golden Confectionary, Super da dai duk kamfanonin da muke amfani da kayansu da su dawo da farashin fulawa zuwa Naira 9,000 ko mu tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani.”

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, mun yi kokarin tuntubar kamfanin BUA na Kano sai dai hakarmu ba ta cimma ruwa ba.

Yayin aikin gargadi

Idan dai ba a manta ba, a makon jiya ne kungiyar ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki uku da ta shiga.

Shugabar Kungiyar, Fatima Auwalu, ta ce a yanzu masu gurasa asara suke yi maimakon su samu riba, saboda hauhawar farashin fulawa, wadda ita ce babbar mahadin sarrafawa a samar da gurasar.

“Tun bayan da muka janye yajin aikin gargadi da muka shiga, mun yi tsammanin masu kamfanonin fulawar za su rage farashinsu, a maimakon haka sai dai ma farashin ya kara hauhawa.

“Yajin aikin gargadi na kwana uku da muka shiga ya jefa mu masu sana’ar gurasa da kwastomominmu cikin mawuyacin hali.

“Babu wani abu da za mu iya yi, dole sai mun sake shiga yajin aikin, don ta haka ne kawai za mu ja hankalin hukuma ta yadda za a yi wa tufkar hanci,” inji ta.

Fatima Auwalu ta kara da cewa, Kungiyarsu ta masu Gurasa ta janye wancan yajin aiki ne saboda shiga tsakanin da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano da wasu hukumomi suka yi.