✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu hakar ma’adinai sun nesanta kan su da ’yan bindiga

Shugaban Kungiyar Masu Hakar Ma’adinai ta Najeriya (MAN), Kabir Kankara, ya bayyana cewa masu hakar ma’adinan ba su da wata alaka da ’yan bindiga. Kankara…

Shugaban Kungiyar Masu Hakar Ma’adinai ta Najeriya (MAN), Kabir Kankara, ya bayyana cewa masu hakar ma’adinan ba su da wata alaka da ’yan bindiga.

Kankara ya bayyana hakan ne a bayaninsa kan haramcin da Gwamnatin Tarayya ta sa kan ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara sakamakon karuwar ayyukan yan taadda.

“A iya sanina, mambobinmu ba su da wata alaka da yan bindiga kuma muna goyon bayan matakin na Gwamnatin Tarayya don dakile rashin tsaro a Zamfara.

“Tabbas ayyukanmu na hakar maadanai suna gudana ne a cikin daji amma ba mu da wata alaka da yan fashi, mu dai muna cikin wadanda lamarin ya shafa ne,” inji shi.

Kankara ya ce matakin magance matsalar rashin tsaro a jihar ya yi daidai domin kare lafiya da rayuka da dukiyoyi.

A ranar Talata Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan hakar ma’adanai da kuma tashin jirage a Zamfara.