✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu halin bera sun hana ruwa gudu a gwamnatin Buhari — Ndume

Buhari mutum ne na gari, sai dai kash masu dan hali suna ci gaba da cin amanarsa.

Sanata Ali Ndume mai wakilcin shiyyar Borno ta Kudu a zauren Majalisar Dattawa na Najeriya, ya ce masu halin bera sun hana ruwa gudu a gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sanata Ndume ya bayyana hakan ne yayin da ya kasance bako a wani shirin Siyasa na ranar Lahadi da gidan talibijin na Channels ya saba daukar nauyi.

Sanatan wanda ya wakilci mazabar Chibok da Damboa da Gwoza a Majalisar Wakilai daga shekarar 2003 zuwa 2011, ya ce masu dan hali a gwamnatin jam’iyya mai ci ta APC na cin amanar manufofi da tsare-tsaren Shugaban Kasa Buhari.

Sanata Muhammad Ali Ndume yayin bayar da amsa dangane da kamun ludayin jagorancin jam’iyyar APC, ya ce Shugaba Buhari mutum ne na gari da babu abin da ya mamaye zuciyarsa face inganta rayuwar talakawan kasar nan.

Sai dai ya ce makarraban gwamnatin Shugaba Buhari sun hana a samu wani ci gaba a kasar nan tare da kawo koma baya a bangaren kyawawan tsare-tsare da manufofi da Shugaban Kasar ya kawo.

“Buhari mutum ne na gari da ya cancanci shugabanci, sai dai kash masu dan hali da suka kasance mafi rinjaye a gwamnatinsa suna ci gaba da cin amanar kyawawan manufofin da shugaban ke son aiwatar wa.”

Ndume ya ce gwamnati mai ci ta kawo muhimman tsare-tsare uku da suka hada samar da ci gaba, yaki da rashawa da kuma samar da ababen more rayuwa kuma duk ciki babu fannin da Shugaba Buhari bai taka rawar gani ba.

Sai dai ya lura cewa aiwatar da wasu manufofin kamar yadda Shugaban Kasar ya bayyana a nan matsalar ta ke.

A cewarsa, Shugaban kasar shi kadai ba zai iya aiwatar da manufofin ba, saboda haka dole ya sanya wakilci a wasu madafun iko daban-daban na gwamnati wanda a haka ne wasu suka fake suna cin dunduniyarsa.