✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu hannu a kisan Gulak za su dandana kudarsu —Buhari

Buhari ya ce tilas ne a hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan Gulak.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce duk masu hannu a kisan fitaccen dan siyasa, Ahmed Gulak a garin Owerri na Jihar Imo za su fuskanci tsattsauran hukunci.

Buhari ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi.

“Ina mai tabbatar da cewar duk wadanda suke da hannu wajen aikata wannan danyen aiki, ba za su gushe ba tare da an hukunta su ba; Za mu yi amfani da duk wata hanya da muke da ita domin gano su tare da hukunta su daidai da laifin da suka aikata.”

Buhari ya bayyana kisan Gulak a matsayin rashin kishi da kuma kawo wa Najeriya koma-baya.

Ya kuma aike da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Gulak, Gwamnatin Jihar Adamawa, abokan arzikin mamacin da daukacin al’ummar Najeriya.