✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu Keke Napep sun fara yajin aiki a Neja

Matuka baburan sun yi barazanar tsunduma yajin-aikin sai baba ya gani.

Fasinjoji sun shiga tasku da sanyin safiyar ranar Litinin a birnin Minna da ke Jihar Neja yayin da matukan babura masu kafa uku, wanda aka fi sani da Keke Napep suka fara yajin aikin gargadi na kwana daya bisa matsin lamba da suke fuskanta daga hukumomi a jihar.

Masu baburan sun kuma toshe hanyar Shiroro da shataletalen Mobil, suna kuma tilastawa duk wani babur mai kafa uku da aka gani tare da fasinjoji ya tsaya, suna kuma neman fasinjojin da su sauka.

Daya daga cikin direban KekeNapep ya ce “Muna fuskantar damuwa gaya a hannun Ma’aikata masu karbar Haraji na Kananan Hukumomin Chanchaga da Bosso dangane da lambar rajistar Karamar Hukumar Chanchaga.

“Suna so a lallai sai an rubuta lambar dara-dara, wanda muke tunanin zai bata mana babur.

“Haka kuma ‘yan sanda, jami’an tsaron hanya da jami’an VIO su ma suna matsa mana ta hanyar karbar kudade kullum.

“Idan aka kama ka aka kai ka ofishinsu, za a sa dole sai ka biya naira dubu biyar kafin su sake ka, abun ya yi yawa,” in ji shi

Wani matukin Keke Napep mai suna Junaidu Abubakar, ya ce za su ci gaba da yajin aikin idan hukumomi sun gaza magance matsalolinsu musamman yadda ‘yan sanda da mutanen wasu hukumomin tsaro ke ci gaba da karbar kudi a hannunsu.

Ma’aji na Jiha na Kungiyar masu babur mai kafa uku, Suleiman Danjuma ya shaida wa Aminiya cewar “Mun farka ne kawai muka ga yajin aikin da mambobinmu suke yi.

“Hakan na faruwa ne saboda yawan harajin da gwamnati ke karba da kuma yawan kama su da hukumar VIO ke yi a kan batun lambar rajistar Karamar Hukumar Chanchaga.

“Ba wai suna adawa da rajistar bane sai dai ba sa son a rubuta ta dara-dara kamar yadda gwamnati take so, tana lalata musu babur,” a cewar Danjuma.

Wasu fasinjojin da suka fito daga Minna ba tare da sun san me ya ke faruwa ba sun samu kan su a wani hali na cunkoso a kan tituna.

Wata mata, Aisha wacce ta ce ta fito daga Paiko don siyan kayan abinci, ta yi kira ga masu yajin aikin da hukumomi da su cimma matsaya saboda talakawa.

“Ban sani ba. Na zo ne kawai daga Paiko. Wannan matsala ce. Ban ma san yadda zan shiga kasuwa ba a yanzu ba,” in ji ta.

Kokarin da Aminiya ta yi na neman karin haske daga bakin Kakakin ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya ci tura.

Haka kuma, neman jin ta bakin Kwamishinar Sufuri ta Jihar, Hajiya Rahmatu Yar’adua bai tabbata ba saboda lambar wayarta ba ta shiga.