✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu neman a sake fasalin kasa basu san me hakan ke nufi ba – Buhari

Ya ce masu neman a raba kasar nan sun jahilci tarihi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce akasarin masu da’awar sauya fasalin kasa ba su ma san me hakan yake nufi ba.

Ya kuma nanata aniyar sa ta tabbatar da ganin Najeriya ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa a karkashin mulkinsa.

Ya bayyana haka ne a sakon da ya aike da shi wajen taron kaddamar da gidauniyar zaman lafiya ta Kudirat Abiola reshen Sabon Gari da aka gudanar a Zariya, Jihar Kaduna.

Shugaba Buhari, wanda Shugaban Hukumar Raba Arzikin Kasa, Alhaji Mohammed Bello Shehu ya wakilta ya ce wadanda suke neman cewa a raba kasar nan ko dai sun jahilci tarihi ko kuma sun jahilci menene yaki.

Ya bayyana cewa mutanen da suka haura shekaru 60 ba za su manta da irin halin da suka tsinci kan su lokacin yakin basasa ba, a don haka ya bukaci wadanda suke jin cewa an musguna musu da su gabatar da korafin su a gaban majalisar dokoki ta kasa.

Wasu daga cikin manyan baki a taron

Ya kuma jaddada aiwatar da dokar baiwa bangaren shari’a da majalisun Kananan Hukumomi ’yancin cin gashin kai,yana jaddada cewa dole Gwamnonin Jihohi su bi doka wajen kau da kai akan kason kudin da gwamnatin tarayya ke baiwa Kananan Hukumomi.

A jawaban da suka gabatar a wurin taron, wakilin gwamnan Jihar Kaduna, kuma Kwamishinan Ilimin Jihar, Alhaji Shehu Mohammed da wakilin Gwamnan Jihar Borno wanda kuma shine Kwamishinan Watsa Labarai da Al’adu na, Alhaji Bubakura Abba Jatau sun ce babu bukatar sake fasalin kasar nan.

Da yake jawabi tun da farko, Shugaban gidauniyar, kuma da ga marigayiya Kudirat Abiola, Alhaji Jami’u MKO Abiola ya ce makasudin kaddamar da gidauniyar shi ne domin a hada kan ’yan Najeriya ba tare da yin la’akari da addini ko kabilanci ba.

Jami'u Abiola a wajen taron gidauniyar wanzar da zaman lafiya tunawa da marigayi Kudirat Abiola reshen Sabon Garin Zariya.
Jami’u Abiola a wajen taron gidauniyar wanzar da zaman lafiya tunawa da marigayi Kudirat Abiola reshen Sabon Garin Zariya.

Ya ce gidauniyar za kuma ta tabbatar da muhimmancin hadin kai da zaman lafiya da ci gaban Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa.

Jami’u Abiola ya ce duk da kasancewar mahaifiyar sa Bayarabiya ce, amma an haife ta kuma ta girma a Arewacin kasar nan inda ta girma a cikin Hausawa kafin daga bisani ta koma Jihar Lagas inda nan ne asalinta.

Ya kara da cewa hakan na nuni da cewa mutum zai iya zama ko wane bangare na kasar nan.

Ya kuma bada tabbacin cewa ayyukan gidauniyar za su fadada har zuwa wayar da kan matasa.