✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Masu rayuwa a karkashin turakun lantarki za su iya fuskantar rashin haihuwa’

TCN ya ce rayuwa a karkashin turakun na da matuƙar hatsari

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya gargadi jama’ar da ke da gine-gine kuma suke rayuwa a karkashin turakun lantarkin da su guji yin hakan saboda barazanar da ke tattare da hakan.

Kamfanin ya kuma yi gargadin cewa masu rayuwa a karkashin wayoyin na cikin barazanar samun matsalar rashin haihuwa, ko ma su kamu da cutar kansa.

Shugaban Kwamitin da ke yaki da gine-gine a kan filayen kamfanin da turakun lantarkin suka wuce ta kai, Kangeh Anengeh Cephas, ne ya bayyana hakan a Kano yayin wata ziyarar neman hadin kai da ya kai wa wasu hukumomin gwamnati da na jami’an tsaro a jihar.

Wuraren da kwamitin ya ziyarta sun hada da Sashen Kula da Filaye na Gwamnatin Jihar da Hukumar Tsaro ta DSS da kuma Hukumar Tsaro ta NSCDC.

A cewar shugaban kwamitin, “TCN ya lura da wata al’ada mai cike da hatsari ta yin gine-gine a karkashi ko kusa da manyan turakun lantarki. Yin hakan na da matukar hatsari kuma yana hana mu gudanar da ayyukanmu a kan turakun.

“Idan tsautsayi ya sa wayar ta yanko ta fado, duk abin da ke karkashinta zai kone kurmus. Sannan kuma tiririn da yake fita daga jikin wayoyin zai iya haifar da cutar kansa, ya sa mata su haifi ’ya’yan da ba sa girma, ko ma ya hana su haihuwar baki daya,” inji shi.

Kangeh, wanda kuma shi ne Manaja mai kula kiyaye lafiya da muhalli na kamfanin ya ce tun da farko an kafa kwamitin ne domin ya tattauna da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar domin ya tattara bayanai sannan ya wayar da kan jama’a kan illar yin hakan.

Daga nan sai ya roki goyon bayan dukkan sassan gwamnati da na jami’an tsaron da ya ziyarta a jihar domin ganin kwamitin ya sami nasara a aikin.

Sai dai ya ce da zarar sun kammala aikin wayar da kan, kamfanin zai fara daukar duk matakin da doka ta tanada kan masu kunnen kashi.