✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu yada kalaman batanci za su biya tarar miliyan 5

Duk gidan rediyo ko talabijin da ya ba da dama aka yi kalaman batanci zai biyar tarar miliyan biyar

Ministan Yada Labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce Hukumar Kula da Gidan Rediyo da Talabijin ta Najeriya (NBC) ta kara yawan tarar da za a ci duk gidan rediyo ko talabijin da ya ba da kafar yin kalaman batanci zuwa Naira miliyan biyar.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen bukin kaddamar da sabon kundin dokokin yada labarai bugu na shida ranar Talata.

Hukumar ta hukunta gidajen kafofin yada labarai 31 wadanda suka yi karya a game da COVID-19 da kalaman kiyayya da sauransu.

Alhaji Lai ya ce an yi karin tarar ne daga N500,000 zuwa miliyan biyar saboda rashin bin doka da gkafofin yada labaran suka yi yayin manyan zabukan shekarar 2019.

“A lokacin zaben na 2019, idan ’yan siyasa suka tunkari kafofin yada labarai da batancin da suke son yi a kan wasu aka ki sanyawa, sai su biya kudin da za a biya tarar ta N500,000 har da riba.

“Duk da miliyan biyar din da muka kara, idan kafar watsa labarai ta biya amma ba ta daina bayar da damar yin kalaman batanci ba, to ba mu da wani zabi sai mu kwace lasisin su”, inji shi.

Ya ce canje-canjen da aka samu a sabon kundin dokokin yada labaran dai sun fi yawa ta fannin harkokin siyasa da labaran gida da tallace-tallace da kuma hana gasa.

A baya dai an zargi gwamnati da yunkurin amfani da dokokin hana kalaman batanci don haramta wa masu suka da ’yan adawa damar fadin albarkacin bakinsu.