✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu zanga-zangar #EndSARS sun kona gidan talabijin na TVC

Fusatattun masu zanga-zangar EndSARS sun banka wa gidan talabijin na TVC da ke Legas wuta. Wani ma’aikacin kamfanin ya ce ‘yan daba sun kai wa…

Fusatattun masu zanga-zangar EndSARS sun banka wa gidan talabijin na TVC da ke Legas wuta.

Wani ma’aikacin kamfanin ya ce ‘yan daba sun kai wa ofishin gidan talabijin din da ke Ikosi hari.

TVC mallakin jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ne.

Ma’aikacin ya ce da safiyar Laraba ne aka kai wa wurin hari tare da banka masa wuta lamarin da ya jefa ma’aikata cikin tashin hankali.

“Gaskiya ne. An banka wa motocin da ke harabar ofishin wuta.

“An riga an katse babban shirinmu na safe’ Your View da ake gudanarwa a lokacin da aka kai harin” inji wani ma’aikacin gidan talabijin din da jaridar Premium Times ta ruwaito.

In ba a manta ba a ranar Litinin masu zanga-zangar EndSARS sun kona ofishin gidan talabijin na AIT da ke Benin Jihar Edo.