✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zanga-zangar #EndSARS sun fantsama a titunan Abuja

Ana zanga-zangar ne saboda cika shekara daya da #EndSARS.

Wasu masu zanga-zanga sun fantsama wasu titunan Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Laraba don tunawa da shekara daya da gudanar da zanga-zangar #EndSARS.

Masu zanga-zangar dai sun taru ne a sansanin Unity Fountain da ke Abuja, kafin su fantsama kan tituna.

Daga cikin masu zanga-zangar, har da mawallafin jaridar nan ta intanet, Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Sowore dai ya yi musu jawabi yayin da su kuma suke dauke da kwalaye.

Sai dai an ga jami’an tsaro a kusa da masu zanga-zangar lokacin da suka bar sansanin inda suka hari Majalisar Dokoki ta Kasa.