✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zanga-zangar neman Buhari ya sauka sun fara kone-kone a Abuja

Hanyar dai ita ce take zuwa har filin jirgin sama na Abuja.

Wasu masu zanga-zangar neman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga kan mulki wato ‘Buhari Must Go’ sun fara kone-kone a kan titin Umaru Musa ’Yar’adua dake Abuja a ranar Litinin.

Hanyar dai ita ce take zuwa har filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abujan.

Lamarin dai ya kawo tarnaki ga masu ababen hawan da ke kokarin wucewa ta kan babbar hanyar.

Masu zanga-zangar dai sun rika rera wakokin ‘Dole Buhari ya sauka’ da kuma daukar kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce iri-iri.

Hakan ya tilasta wa masu ababen hawa tafiya a hankali saboda kaucewa wutar da aka kunna a tsakiyar titi.

Ko a rabar 12 ga watan Yunin 2021 sai da aka gudanar da makamanciyar irin wannan zanga-zangar a Abuja, amma daga bisani an kama kusan dukkan masu hannu a cikinta.

Daga bisani, jagoran masu fafutukar #RevolutionNow, Omoyele Sowore ya saka hotuna da bidiyon masu zanga-zangar a shafukan sada zumunta.