✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata 11,200 aka yi wa fyade a Najeriya a 2020 —Amnesty Int’l

Mata da kananan yaran da ake wa fyade ba sa samun adalci, masu laifin kuma na ci gaba da aikatawa

Mata da kananan yara akalla 11,200 ne aka yi wa fyade a Najeriya a shekarar 2020, a cewar wani rahoto.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ce ta ba da alkaluman a sabon rahotonta kan fyade da cin zarafin mata da kananan yara.

Rahoton da kungiyar ta fitar a ranar Laraba, ya ce, “Najeriya ta yi watsi da mata da kananan yara ta yadda ba sa iya samun adalci, masu aikata laifin kuma an bar su suna ci gaba da aikata wannan danyen aiki na tauye hakki.”

Gazawar gwamnati wajen daukar mataki da hukunta masu aikata fyade ya sa wadanda aka yi wa ba sa fitowa su kai kara, inji rahoton mai taken, “Najeriya: Fadi-tashin neman adalci ga mata da kananan yaran da aka yi wa fyade.”

Kungiyar ta fitar da rahoton ne bayan binciken da ta gudanar tsakanin watan Maris na 202 zuwa watan Agustan 2021 a kan kararrakin fyade da cin zarafin mata da kananan yara, ciki har wata mai shekara shida da mai shekara 11 da aka yi musu danyen aikin.

Binciken ya gano cewa rashin daukar kwararan matakan magance matsalar fyade da cin zarafin mata daga bangaren gwamnati ya sa matsalar na ta karuwa, masu aikata laifukan kuma na kara tsaurin ido a Najeriya.

“Wadanda aka yi wa fyade ba sa samun adalci, ba a gurfanar da wadanda ake zargi, akwai kuma daruruwan laifukan fyade da ba a bayar da rahotonsu saboda tsoron muzantawa ko dora laifin a kan wadanda aka yi wa fyade, sannan akwai batun rashawa.

“Ba a dauki tsuraran matakai ba don magance matsalar yadda ya kamata ba a Najeriya.

Daraktan Amnesty International a Najerriya, Osai Ojigho, ta kara da cewa, tsoron a dora wa matan da aka yi wa fyade laifin abin da ya same su ko karyata su ya hana yawancinsu kai kara, ballanta maganar neman samun adalci.

“Duk da cewa hukumomin Najeriya sun ayyana dokar ta baci a kan cin zarafin mata da aikata fyade, ana ci gaba da aikata laifujan a mataki mai tayar da hankali,” inji rahoton.