✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata 5 da Saudiyya ta taba nadawa mukamin Jakadanci a kasashen waje

A tarihin Masarautar Saudiyya wadannan mata suka fara rike mukamin jakadancin kasar.

A kokarin da Gwamnatin Saudiyya ke yi na karfafa wa mata da kuma damawa da su a harkokinta ya sanya kasar ta nada wasu mata su biyar a matsayin jakadunta a sassan duniya.

Wannan bangare ne na kudurin da Yarima Mohammed Bin Salman ke da shi na son bunkasa kasar ya zuwa 2030.

Wadannan mata sun hada da:

  • Gimbiya Reema bint Bandar Al Saud
Reema

Ita ce ta zama mace Jakadiya ta farko ga kasar a 2019 bayan da Yarima Mohammed bin Salman (Mataimakin Sarki a wancan lokaci) ya nada ta Jakadar Masarautar Saudiyya a Amurka.

Reema ta rike mukamai daban-daban a Masarautar, kuma ‘yar gwagwarmayar son ci gaban rayuwar ‘yan uwanta mata ce.

Mahaifinta, Yarima Bandar bin Sultan, ya taba zama jakadan Saudiyya a Amurka daga 1983 zuwa 2005.

  • Haifa al-Jadea
Haifa

An nada Haifa al-Jadea a matsayin Jakadiya kuma shugabar tawagar Masarautar a Tarayyar Turai da Kungiyar Makamashin Nukiliya ta Turai (EAEC) a ranar 3 ga watan Janairu, 2023.

Ta yi karatu mai zurfi, kuma ‘yar jarida ce kuma kwararriya a fannin sasanta rikiciki tsakanin kasashe da kuma fannin mu’amala a tsakanin kasashe.

Ita ma ta yi aiki a wurare da dama, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya.

  • Inas al-Shahwan
Inas
Inas

A watan Afrilu, 2021 aka rantsar da Inas al-Shahwan a matsayin Jakadiyar Saudiyya. Ita ce ta uku a jerin matan da Saudiyya ta nada jakadunta, ta yi wa kasarta jakadanci ne a kasar Sweden.

Ita ma ta yi karatu mai zurfi, kuma kwararriya ce a fannin kawancen kasa da kasa.

Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Saudiyya na daga cikin wuraren da Inas ta yi aiki da sauransu.

  • Nisreen al-Shibel
Nisreen

Nisreen bint Hamad al-Shibel ta zama jakadiya ce a ranar 3 ga watan Janairu, 2023 inda  ta wakilci kasarta a Finland.

Jim kadan bayan rantsar da ita, Nisreen ta shiga shafinta na Twitter inda ta wallafa sakon godiya ga masu ruwa da tsaki, tare  yabo dangane da damar da aka ba ta don yi wa kasarta aiki.

  • Amal Yahya al-Moallimi
Amal

Ta zama jakadiyar Saudiyya ce a 2020, inda ta wakilci kasarta a kasar Norway.

Ita ce ta uku daga jerin matan da suka yi wa Saudiyya jakadanci.

Ta yi karatu mai zurfi, kuma kwararriya ce a Harshen Ingilishi da kuma fannin yada labarai.

Ta yi aiki a Hukumar Kare Hakkin Dan Adam da sauran wurare.