✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata dubu: An daure mai wa’azi shekara dubu

Wata kotun kasar Turkiyya ta daure wani mai malami mai suna Adnan Oktar sama da shekara dubu a kurukuku bayan kama shi tare da wadansu…

Wata kotun kasar Turkiyya ta daure wani mai malami mai suna Adnan Oktar sama da shekara dubu a kurukuku bayan kama shi tare da wadansu mutum 200 da ake zargi da cin zarafin mata.

An kama wadanda ake zargin ne kewaye da matan da ke shigar tsaraici kuma yake kiransu da suna ’ya’yan kyanwa.

An tuhumi Adnan Oktar da auren mata dubu da kuma yin wa’azin bautar halittu da addinin gargajiya yayin da matan ke zagaye da shi cikin tsiraici.

Hukumomin Turkiyya sun ce  mafi yawan matan da suke tare da shi an yi musu sauyin halitta ne daga maza zuwa mata ta hanyar yi musu tiyata.

An kama su ne suna rawa a zagaye da shi bayan an sanya musu kida a dakin da ake kirkiran kida na gidan talabijin dinsa.

Malamin mai shekara 64 wanda aka tsare tun a 2018 tare da wadansu da ake zargin masu aikata laifi ne, ’yan sandan birnin Instanbul na sashen binciken masu aikata laifuffukan masu alaka da kudi ne suka kama su.

An yanke masa hukuncin daurin shekara 1,075 sakamakon laifuffukan da suka hada da: cin zarafin mata da kananan yara da damfara da shiga rigar siyasa ko na jami’an soji; Kamar yadda wani dan jaridar NTB ya ruwaito.

Kotun ta kuma yanke wa wadansu wadansu manyan jami’an kamfanin Oktar biyu hukuncin daurin shekara 211 da kuma shekara 186.

Jami’i a Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu ya ce, an samu Oktar da karin laifuffuka kan taimakon wata kungiya ta dan asalin Turkiyya mazaunin Amurka Fethullah Gulen wanda kasar Turkiyya ta dora wa laifin  yunkurin juyin mulki a shekarar 2016.

Sai dai Adnan ya musanta cewa yana da alaka da Gulen sannan ya yi martani kan rahoton cewa yana da kungiyar matsafa da take kunshe da mata, inda ya ce: “Wannan bakon abu ne ban san da shi ba”

Majiyar Anadolu ta ruwaito cewa mutum 236 da ke kare Adnan za a ci gaba da tuhumar su, yayin da za a ci gaba da tsare mutum 78 har zuwa lokacin zartar musu da hukunci.

Adnan Oktar ya bayyana wa alkalin kotun cewa a watan Disamba yana da kawayensa mata da suka kai kusan dubu, kuma wannan ne ya sa aka yanke hukuncin wadannan mata ya mayar da su matansa ne.