Mata miliyan 37 ne ba sa samun audugar al’ada a Najeriya | Aminiya

Mata miliyan 37 ne ba sa samun audugar al’ada a Najeriya

Audugar mata. Hoto: Bustle.com
Audugar mata. Hoto: Bustle.com
    Rosemary Etim Bassey, da Rahima Shehu Dokaji

Yayin da ake bikin Ranar Kula da Lafiyar Mata Yayin Al’ada ta 2022, wata kididdiga daga kungiyar kasa da kasa ta PLAN International ta nuna fiye da mata miliyan 37 ne a Najeriya ba sa samu ingantattun kayayyakin al’ada saboda tsadarsu.

Kungiyar ta PLAN International bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na kwana guda da ta shirya, domin bikin ranar.

A don haka ne kungiyar ta bukaci a raba audugar al’adar ga ’yan mata kyauta, domin rage kaifin matsalar.

A nata bangaren, wakiliyar ministar mata, Ekanem Gloria, ta ce ma’aikatar na sane da ayyukan kungiyar a kokarinta na rage matsalolin al’ada da mata ke fama da shi a Najeriya.

Daraktan Kungiyar ta PLAN International, Dokta Charles Usie, ya ce jinin al’ada ba larura ba ce ko wani abin kunya, don haka akwai bukatar daina boye-boyen da ake yi a kai domin rage kyamar da mutane ke nunawa a kai.

Ina Mafita?

Ya ce: “Lokacin da cutar AIDS ta bulla, dole haka muka ajiye kunya muka dinga yayata maganar ba da kororon roba kyauta, kasancewar amfani da shi na daya daga cikin hanyoyin dakile ta”, in ji shi.

“Lokaci ya yi da ya kamata ita ma audugar matar mu ci gaba da yayata amfani da ita, har zuwa lokacin da za a koma rabawa kyauta ga ’yan mata”.

Mista Usie ya ce, “Babu yadda za a yi ka kalli rayuwar matashiyar mace ba ka sako batun tsafta yayin al’ada ba;

“Don haka a yau kamar kowacce shekara, muna tare da dukkanin matan Najeriya da ma na duniya, kuma muna jaddada cewa lafiyar mace mai al’ada ba a iya kanta ta tsaya ba, a’a ta shafe mu duka”.