✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata sun ci gaba da karatun jami’a a Afghanistan

Karon farko ke nan da dalibai mata ke ci gaba da karatu a jami'o'i a Afghanistan tun bayan da Taliban ta karbe mulkin kasar a…

Dalibai mata sun ci gaba da halartar jami’o’i a kasar Afghanistan a ranar Laraba, bayan an bude makarantu a kasar a karkashin mulkin gwamnatin Taliban.

Hukumomi sun ce an ci gaba da daukan darussa a jami’o’in da ke lardunan Laghman, Nangarhar, Kandahar, Nimroz, Farah da kuma Helmand a safiyar Laraba, kuma za a ci gaba da karatu ne ta hanyar raba tsakanin ajin mata da na maza a jami’o’in.

Sun kara da cewa nan gaba kuma a cikin watan Fabrairun da muke ciki za a sanar da lokacin bude jami’o’in da ke sauran sassan kasar.

Karon farko ke nan da dalibai mata ke ci gaba da karatu a jami’o’i a Afghanistan tun bayan da Taliban ta karbe mulkin kasar a watan Agustan 2021.

Wani dalibi da ke karatu a fannin shari’a a jami’a, Zarlashta Haqmal, ya ce, “Abin farin ciki ne ganin yadda aka ci gaba da karatu, amma muna tsoron kada Taliban su sake hana mata zuwa makaranta.”

Tun bayan karbar mulkin Taliban a Afghanistan aka rufe wasu makarantu da jami’o’i mallakar gwamnati,  matakin da ya haifar da fargabar cewa gwamnatin za ta sake haramta wa mata zuwa makarantu kamar yadda ta yi a lokacin mulkinta na baya a tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.

Masu sharhi sun ce sake bude jami’o’in wani babban mataki ne da gwamnatin Taliban ta dauka domin samun karbuwa da kuma goyon baya daga kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce, dalibai mata da takwarorinsu maza sun halarci darussa a Jami’ar Laghman a safiyar Laraba, duk da cewa dalibai ba su je da yawa ba yadda aka saba a baya.

AFP ya ruwaito cewa an ga jami’an tsaron Taliban dauke da manyan bindigogi suna gadi a kofar shiga jami’ar a safiyar Laraba.