✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mata ta kwara wa mijinta acid bayan takaddama a tsakaninsu

Lamarin dai ya faru ne bayan wata ’yar takaddama a tsakaninsu.

Wata mata ta kwara wa mijinta acid a jiki bayan wata ’yar takaddama da ta shiga tsakaninsu a Benin, babban birnin Jihar Edo.

Matar, mai suna Becky, ta kwarara wa mijin nata mai suna Odion acid din ne a jiki bayan rashin jure sabanin da suka samu a tsakaninsu.

Sabanin dai ya kai su zuwa ofishin ’yan sanda domin yi masu sulhu, inda aka sasanta su, tare da rokonsu da su zauna lafiya a kodayaushe.

Sai sai duk da wannan sasancin, da alama matar ba ta hakura, ba inda bayan dawowar su gida ta kwarara masa acid din a jiki ba tare da ya yi aune ba.

Mazauna yankin sun shaida wa wakiliinmu cewa ihun magidancin suka ji suka shiga gidan ma’auratan domin kai dauki,  wanda a nan ne suka ga wannan abin tashin hankalin.

A halin yanzu dai an mika matar zuwa ga hannun ’yan sanda domin ta girbi abin da ta shuka.

Ko da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan kan lamarin, sai kakakinsu a Jihar ya ce za su yi bayanai bayan sun kammala gudanar da bincike.