✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata ta maka mijinta gaban kotu a Gombe bisa zargin duka da cizo

Wata matar aure a Jihar Gombe ta maka mijinta a kotu kan zargin duka da cizon da ta ce yana yi mata a duk lokacin…

Wata matar aure a Jihar Gombe ta maka mijinta a kotu kan zargin duka da cizon da ta ce yana yi mata a duk lokacin da suka samu sabani a tsakaninsu.

Matar, mai suna Lawiza Mu’azu da ke zaune a Unguwa Uku a Gombe, ta gurfanar da mijin nata, Alhaji Mu’azu, a gaban kotun masu aikata manyan laifuffuka da ke unguwar IDI a Jihar.

Matar dai ta shaida wa kotun cewa mijin ta yana yawan dukan ta a lokuta daban-daban idan sabani ya shiga tsakaninsu.

Ta ce sabanin da suka samu da mijin nata a kwanan baya shi ne na kin yin girki a gidan, inda ta ce kuma hakan ya faru ne saboda rashin makamashin da bai samar musu a gidan ba.

“A lokacin da ya yi min dukan farko, na tafi gidanmu, sai mahaifina ya sa ni na dawo, daga baya sai mijina ya cijeni bayan dukan da ya yi min, ya gatsa min dan yatsa wai saboda rashin girkin da ban yi ba,” inji Lawiza.

Daga ta roki kotun da ta raba aurenta da mijin saboda ta ce ba za ta iya ci gaba da lamuntar hakan ba.

Sai dai mijin ya musanta zargin da matar take masa, inda ya ce ba ya dukanta, kuma bai cije ta ba.

Ya ce taki yin girki ne har na tsawon mako guda, wanda hakan a cewarsa ya saba ka’ida.

Mu’azu, ya kara da cewa a sanadiyyar hakan ne ya sa daya matarsa, Jummai, ta hana ita Lawizan abincin da ta girka.

“A boren ta na an hana ta abinci da Jummai tayi ne ya sa ita Lawiza, ta rike ni tana neman ’yancin ta, har ta sa min hannu a aljihu za ta dauki kudi da karfi. Inda a sanadiyar haka ne rikici ya shiga tsakaninmu amma ni ban cije ta ba” inji shi.

Daga nan ne sai Alkalin kotun, Mai Shari’a Garba Abubakar, ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar Litinin, 24 ga watan Janairun don ba mai kara damar gabatar da shaidun ta a gabanta.