✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mata ta nemi kotu ta hukunta mijinta kan yi wa karamar ’yarsu fyade

Kotu ta tura mutumin da ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 10 fyade zuwa gidan yari

Wata matar aure ta bukaci kotu ta ladabtar da mijinta kan yi wa ’yar cikinsa da suka haifa mai shekara 10 fyade.

Matar ta bukaci haka ne bayan ta kai wa Kotun Majistare da ke zamanta a Ogba, Jihar Legas, karar mijin nata kan abin da ta kira dabbanci.

DAGA LARABA: Yadda Yi Wa Kananan Yara Fyade Ya Yadu A Arewacin Najeriya

Mutum 13 sun kone kurmus a hatsarin mota a Kano

Matar mai shekara 35 ta roki kotun da ta yi wa mijinta tsattsauran hukunci kan aika-aikan da ya yi wa ’yar cikinsa a lokacin da ita ba ta nan.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Akeem Raji, ya shaida wa kotu cewa “Wanda ake zargin ya yi barazanar kashe ’yarsa idan ta gaya wa mahaifiyarta.”

Ya ce amma da yarinyar ta kasa jure radadi bayan abin da uban ya yi mata, sai ta gaya wa mahaifiyarta.

Ya kara da cewa kafin zakke wa yarinyar da karfin tuwo, sai da uban nata ya kulle ta a daki ya tilasta mata tsotsar gabansa.

Ya bayyana cewa magidancin ya yi wa ’yar cikinsa fyade ne a unguwar Lekki da ke jihar ta Legas.

Yanzu magidancin na fuskantar laifukan fyade da ke iya ja masa daurin shekara 14.

Alkalin kotun, B. O. Osunsanmi ta sa a tsare shi a Gidan Yari na Kirikiri zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba.

Ta ba da umarnin ne bayan masu kara sun nemi karin lokacin bincike da kuma shawara daga Ofishin Gurfanar da Laifuka na Jihar Legas.